• English
  • Business News
Thursday, October 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ƙasashen Larabawa Da Musulmai Sun Yi Allah Wadai Da Hare-haren Isra’ila A Zirin Gaza

bySulaiman
2 years ago
Gaza

Taron Haɗin Guiwar Ƙasashen Larabawa da sauran ƙasashen Musulmai, ya yi tir tare da nuna rashin amincewa kan hare-haren da sojojin Isra’ila ke ci gaba da kaiwa a Gaza.

Taron wanda aka gudanar ranar Asabar, 11 ga Nuwamba, ya bayyana cewa abin da sojojin Isra’ila suka yi laifin tsallake ƙa’idoji da sharuɗɗan yaƙi ne, kuma dabbanci ne kan Falasɗinawa fararen hula.

  • Tattalin Arzikin Sin Na Kan Hanyar Kai Kasar Ga Cimma Burikanta Na 2023
  • Hukumar Kwastam Ta Kama Kwayoyin Tramadol Na Biliyan N3.55bn A Legas

Ministan Yaɗa Labarai, Mohammed Idris ne ya tabbatar da haka, a cikin wata sanarwar da Jami’in Yaɗa Labarai na ministan, Rabi’u Ibrahim ya fitar.

Idris, wanda ya na cikin tawagar Shugaban Ƙasa Bola Tinubu a wurin taron, ya ƙara da cewa, an kuma yi kira da a gaggauta gudanar da gagarimin taron duniya, inda za a bijiro da hanyoyin tabbatar da wanzuwar zaman lafiya a yankin Falasɗinu.

Sanarwar bayan taron da wanda shugabannin ƙasashen Ƙungiyar OIC da na Majalisar Ƙasashen Larabawa suka halarta, an yi kira da a gaggauta tsagaita dukkan hare-haren da sojojin Isra’ila ke kaiwa a yankin Gaza.

LABARAI MASU NASABA

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

Kuma sun fito ƙarara sun ce farmakin da Isra’ila ke kaiwa kan Gaza ci gaba ne da irin mamayar da ta yi wa Falasɗinawa a 1967 a yankin Gaza, West Bank, Al-Quds Al-Sharif da kuma Arewacin Jerusalem.

Sannan kuma taron ya buƙaci Majalisar Ɗinkin Duniya ta fito da ƙwaƙƙwarar matsaya a ƙarƙashin Majalisar Tsaro ta Majalisar Ɗinkin, wadda za ta tilasta daina duk wani nau’i da salo na gallazawa da Isra’ila ke yi wa Falasɗinawa.

Haka nan kuma wannan taro ya nemi Isra’ila ta kawo ƙarshen mamayar da ta ke yi a yankin, domin ya karya ƙa’ida da iyakokin da dokokin ƙasa da ƙasa suka shar’anta.

Sun ce musamman farmakin ya saɓa wa ƙa’idar Majalisar Ɗinkin Duniya mai lamba AES-101.25, ta ranar 26 ga Oktoba, 2013.

A wurin taron, shugabannin sun yi kakkausan kira ga Majalisar Tsaro ta Majalisar Ɗinkin Duniya cewa “ta gaggauta yin Allah-wadai da dabbacin da sojojin Isra’ila ke kan yi na ruguza asibitoci a Zirin Gaza. Kuma ta yi tir kan hana a shigar wa Falasɗinawa da magunguna, abinci fetur da katse wutar lantarkin da mahukuntan Isra’ila ɗin suka yi a Zirin Gaza.”

An zartas da cewa matuƙar Majalisar Ɗinkin Duniya ta ƙi yin tir da dabbancin da sojojin Isra’ila ke aikatawa a Zirin Gaza, to tamkar ta halasta mummunan kisan da ake wa fararen hula ne da suka ƙunshi ƙananan yara, dattawa, mata da kuma ruguza Gaza da ake kan yi.

Sun ce ya zama wajibi Isra’ila ta ɗage takunkumin datse Zirin Gaza da ta yi, tsawon shekaru masu yawa.

Sannan kuma taron ya yi tir dangane da yadda wasu ƙasashe suka riƙa taimaka wa Isra’ila da muggan makaman da take amfani da su, ta na kisan gilla kan Falasɗinawa, tare da ruguza masu gidaje, asibitoci, makarantu, masallatai, coci-coci da sauran wuraren more rayuwa.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace
Labarai

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025
Tinubu
Manyan Labarai

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025
Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa
Labarai

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

October 8, 2025
Next Post
Gobara

Gobara Ta Kone Fiye Da Masaukai Dubu A Sansanin Gudun Hijira Na Borno

LABARAI MASU NASABA

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025
Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

October 8, 2025
Tinubu

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025
Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

October 8, 2025
Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

October 8, 2025
Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

October 8, 2025
Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Go to mobile version