Ran 15 ga wata bisa agogon wurin, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da takwaransa na kasar Amurka Joe Biden a rukunin gidajen alfarma na Filoli dake birnin San Francisco na kasar Amurka. Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya yi wa manema labarai bayyani bayan taron.
Ya ce, ban da ganawar da shugabnanin biyu za su yi yayin taron APEC, shugaba Joe Biden ya gayyaci shugaba Xi Jinping don ganawa ta musamman a tsakaninsu a wannan karo, kuma shugabannin biyu sun tattauna yadda ya kamata. Ana iya cewa, wannan ganawa na da ma’ana da muhimmanci matuka.
- Yanzu-yanzu: Kotun Daukaka Kara Za Ta Yanke Hukunci Kan Karar Zaben Gwamnan Kano Gobe A Abuja
- Mutane 32 Sun Mutu A Wani Sabon Hatsarin Kwale-kwale A Jihar Taraba
Ban da wannan kuma, ya ce, shugabannin biyu sun gana a wani muhimmin lokaci na huldar kasashen biyu. Kasashen duniya na matukar bukatar huldar kasashen biyu mai inganci. Ganawar ta wannan karo ta aza wani tubali mai kyau ga dangantakar kasashen biyu da ma abu mai muhimmanci ga huldar kasashen duniya.
An shafe sa’o’i 4 ana gudanar da wannan ganawa, inda shugabannin biyu suka yi musanyar ra’ayoyi mai zurfi da ba da shawara kan yadda bangarorin biyu za su cimma ra’ayi na gaskiya da daidaita bambanci da ingiza hadin kai da shawarwari tsakaninsu, tattaunawar da suka yi ya shafi rikici tsakanin Palasdinu da Isra’ila da rikicin Ukraine da sauyin yanayi da na’urori masu sarrafa kansu da dai sauransu. Kazalika sun tabbatar da nauyin dake wuyansu a duniya da samar da makomar hadin kai.
Dadin dadawa, Wang Yi ya ce, a yayin ganawar, shugaba Xi Jinping ya gabatar da matsayin da Sin ta dade take dauka kan huldar dake tsakaninsu. Wato Sin da Amurka abokan juna ne, ya kamata kasashen biyu sun hada kansu kan bangarorin da suka dace da muradunsu, yana mai fatan Amurka za ta zabi hanyar da ta dace don bunkasa huldarsu yadda ya kamata.
Na biyu, mutunta juna da zama tare cikin lumana da hadin kai da cin moriya tare.
Na uku, Sin da Amurka su cimma matsaya daya kan dangantakarsu, don daidaita mabambancin ra’ayi tsakaninsu da ciyar da hadin kansu gaba da sauke nauyin dake wuyansu tare da ingiza mu’ammala a fannin al’adu tsakaninsu.
Sannan, a yayin wani taron manema labarai da aka shirya a yau Alhamis, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Mao Ning ta bayyana cewa, shugaba Xi Jinping da takwaransa na Amurka Joe Biden sun yj tattaunawar keke da keke mai zurfi a jiya Laraba, kuma hanyar da ta dace da kyautata dangantakarsu, ta kara fayyace nauyin dake wuyan manyan kasashen tare da samar da “burin San Francisco” domin kyautata makomarsu.
A cewar Mao Ning, wannan kyakkyawar ganawa ce mai ma’ana dake da muhimmiyar tasiri mai kyau. Tana mai cewa, batu ne mai muhimmanci ga duniya, haka kuma nasara ce ga tarihin dangantakar kasashen biyu.
Mao Ning ta jaddada cewa, tattaunawa da hadin gwiwa ita ce kadai zabi mai kyau ga kasashen biyu. Kuma ya kamata tattaunawar ta San Francisco ta zama mafarin kyautata dangantakarsu. Bugu da kari, akwai bukatar bangarorin biyu su karfafa tubalin dangantakarsu, da gina ginshikin hulda da juna cikin aminci da karko kuma bisa alkibla mai dorewa. (Masu Fassarawa: Amina Xu, Faiza Mustapha)