Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa, gwamnatinsa ta gaji mummunan bashi daga gwamnatin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, wanda ya koka cewa Nijeriya na da babban gibi na rasha kayayyakin more rayuwa da kuma na harkokin noma.
Shugaban kasan ya ce wannan ba uzuri ba ne, amma dai gwamnatinsa ta gaji mummunan bashi.
- Gwamnatin Kano Ta Yi Kira A Kwantar Da Hankali Gabanin Hukuncin Kotun Daukaka Kara
- Yanzu-yanzu: Kotun Daukaka Kara Za Ta Yanke Hukunci Kan Karar Zaben Gwamnan Kano Gobe A Abuja
Ya bayyana hakan ne a daren ranar Litinin, a birnin Makkah na kasar Saudiyya, yayin da yake tattaunawa kan cibiyoyi masu samar da ababen more rayuwa na biliyoyin daloli daga bankin ci gaban Musulunci, don samar da ababen more rayuwa a matakai daban-daban a Nijeriya.
Mai magana da yawun shugaban kasa, Ajuri Ngelale shi ya bayyana wannan tattaunawa a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talata.
Ya ce wannan lamari ya samo asali ne sakamakon tattaunawa mai muhimmanci na saka hannun jari tsakanin Shugaba Tinubu da mataimakin shugaban bankin raya Musulunci, Dakta Mansur Muhtar, bayan dawowar shugaban kasa daga Sallar Magariba.
“Nijeriya ita ce fitilar da ke haska haska hanya ga Afirka. Kuma da zarar Afirka ta haskaka, duniya za ta zama wuri mafi haske ga dukkan Bil’adama. Mun kuduri aniyar samar da makoma ga matasanmu masu hazaka. Zuba jari a Nijeriya zai kasance mafi samun yawan riba a duniya. Kudaden masu zuba jari za su rika tafiya cikin sauki a ciki da wajen kasarmu. Tsarin zai zama mai kyau. Kuma bankinku ya kasance amintaccen abokin tarayya na ci gaba.
“Muna da babban gibi a bangaren ababen more rayuwa na tashar jiragen ruwa, samar da wutar lantarki, da kayayyakin aikin gona da za su ba da damar samar da abinci mai dorewa a kasarmu. Za mu yi kokarin cike wadannan gibin ga masu zuba jari.
“Mun gaji mummunan bashi daga magabata. Ba mu da wani uzuri. Akwai sassa da yawa cike da damar saka hannun jari ga ‘yan kasuwa. Muna son habaka dangantaka a tsakaninmu domin cimma burinkanmu,” in ji shugaban.