• English
  • Business News
Friday, October 24, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Karancin Ruwan Sama A Nijar: Wasu Manoma Sun Koma Hakar Zinari

by Rabi'u Ali Indabawa
2 years ago
Manoma

Kashi 40 cikin 100 na Manoma a Jihar Agadas da ke Arewacin Jamhuriya Nijar sun kaurace wa gonakinsu, inda suka koma hakar neman zinari bayan da suka samu kansu a halin tsaka mai wuya sakamakon matsalar karancin ruwan sama da aka samu a bana.

Masana sun yi gargadin cewa rashin isasshen ruwan sama a Nijar a bana ka iya haifar da karancin abinci da hauhawar farashin kayayyaki a kasuwanni, sai dai gwamnatin kasar ta ce ta na daukar matakai domin magance matsalar.

  • Gimbiya Sirindhorn Ta Thailand:Shawarar “Ziri Daya Da Hanya Daya” Ta Inganta Hadin Gwiwar Al’ummun Kasa Da Kasa
  • Rashin Adalci Ne Karbe Kashi 40 Cikin 100 Na Kudaden Shigar Jami’oi (1)

A bana manoma a Jihar Agadas da ke Arewacin Nijar sun samu kansu a cikin hali na tsaka mai wuya sakamakon karancin ruwan sama da aka fuskanta, lamarin da ya tilasta kusan kashi 40 cikin 100 na manoma barin gonakinsu domin zuwa wuraren hako zinari.

Adam Efangal, shi ne magajin garin yankin Tabelot, ya ce rashin ruwan sama ya shafi harkokin noma, don haka akan tilas manoma suka koma neman zinari.

Babu wani yanki a Jihar Agadas da ake aikin noma da ya tsira daga iftila’in, lamarin da ya sa manoman tafka asara mai yawa, inji Madugu Nuhu, mamba a majalisar manoman Jihar Agadas.

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Kashe ‘Yan Ta’adda 50, Sun Daƙile Hare-Hare A Borno

Harkokin Ciniki Da Zuba Jari Tsakanin Sin Da Afirka Sun Samu Ci Gaba Mafi Girma a Shekaru 5 Da Suka Gabata

A gefe guda kuma, manoma masu yawa na tattare da barazanar rasa amfanin gona sakamakon bullar kwarin da ke lalata amfanin gona, to sai dai tuni hukumomi suka dauki matakin yin feshin magani, a cewar Mahaman Mu’azu, wanda ke kula da manoma a Jihar Agadas.

Domin tabbatar da ganin an samu mafita kan irin matsalolin da manoman suke fuskanta ya sa hukumomin mulkin soja a Nijar ke shirin daukar matakai domin inganta harkokin noma.

Masana dai na gargadi kan yadda matsalar ka iya haifar da karancin abinci da tashin farashi a kasuwanni Nijar da ma wasu kasashen Afrika ta Yamma irinsu Benin, Senegal, da Ibory Coast, duba da cewa kasashen sun dogara da Nijar ne wajen shigar musu da kayan amfanin gona kamar albasa, alkama, da kuma dankalin turawa.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Sojoji Sun Kashe Mayakan Boko Haram 6, Sun Kama Wasu A Borno
Manyan Labarai

Sojoji Sun Kashe ‘Yan Ta’adda 50, Sun Daƙile Hare-Hare A Borno

October 23, 2025
Harkokin Ciniki Da Zuba Jari Tsakanin Sin Da Afirka Sun Samu Ci Gaba Mafi Girma a Shekaru 5 Da Suka Gabata
Ra'ayi Riga

Harkokin Ciniki Da Zuba Jari Tsakanin Sin Da Afirka Sun Samu Ci Gaba Mafi Girma a Shekaru 5 Da Suka Gabata

October 23, 2025
Uwargidan Tinubu Ta Ƙaddamar Da Ɗakin Karatu Na E-learning A Zamfara
Labarai

Uwargidan Tinubu Ta Ƙaddamar Da Ɗakin Karatu Na E-learning A Zamfara

October 23, 2025
Next Post
Sojojin Mali Sun Kwace Muhimmiyar Tungar ‘Yan Tawayen Kidal

Sojojin Mali Sun Kwace Muhimmiyar Tungar ‘Yan Tawayen Kidal

LABARAI MASU NASABA

Fahimtar Sabon Tunani: Samar Da Wadata Ga Dukkan Jama’a Ta Daidaita Gibin Dake Tsakanin Hamshakai Da Matalauta

Fahimtar Sabon Tunani: Samar Da Wadata Ga Dukkan Jama’a Ta Daidaita Gibin Dake Tsakanin Hamshakai Da Matalauta

October 23, 2025
Shugaban Senegal: Kasar Sin Ta Zama Abin Koyi Ga Kasashe Masu Tasowa

Shugaban Senegal: Kasar Sin Ta Zama Abin Koyi Ga Kasashe Masu Tasowa

October 23, 2025
Sojoji Sun Kashe Mayakan Boko Haram 6, Sun Kama Wasu A Borno

Sojoji Sun Kashe ‘Yan Ta’adda 50, Sun Daƙile Hare-Hare A Borno

October 23, 2025
Me Ake Fatan Gani A Shirin Sin Na Raya Kasa Na Shekaru Biyar Biyar Na Gaba

Me Ake Fatan Gani A Shirin Sin Na Raya Kasa Na Shekaru Biyar Biyar Na Gaba

October 23, 2025
Harkokin Ciniki Da Zuba Jari Tsakanin Sin Da Afirka Sun Samu Ci Gaba Mafi Girma a Shekaru 5 Da Suka Gabata

Harkokin Ciniki Da Zuba Jari Tsakanin Sin Da Afirka Sun Samu Ci Gaba Mafi Girma a Shekaru 5 Da Suka Gabata

October 23, 2025
Uwargidan Tinubu Ta Ƙaddamar Da Ɗakin Karatu Na E-learning A Zamfara

Uwargidan Tinubu Ta Ƙaddamar Da Ɗakin Karatu Na E-learning A Zamfara

October 23, 2025
Kungiyar IOMed Za Ta Taka Rawar Gani Wajen Gina Al’umma Mai Makomar Bai Daya 

Kasar Sin Ta Karyata Rahoto Na Zuki-ta-malle Da Wata Cibiyar Binciken Amurka Ta Fitar Game Da Hadin Gwiwar Sin Da Yammacin Afirka

October 23, 2025
An Kammala Taron JKS Inda Aka Amince Da Shawarwari Kan Shirin Ci Gaban Kasar Sin Na Shekaru Biyar-biyar Karo Na 15

An Kammala Taron JKS Inda Aka Amince Da Shawarwari Kan Shirin Ci Gaban Kasar Sin Na Shekaru Biyar-biyar Karo Na 15

October 23, 2025
Tinubu Ya Rantsar Da Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC

Tinubu Ya Rantsar Da Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC

October 23, 2025
Sanarwar Bayan Taron Jks: Mene Ne Sirrin Kwarin Gwiwar Kasar Sin?

Sanarwar Bayan Taron Jks: Mene Ne Sirrin Kwarin Gwiwar Kasar Sin?

October 23, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.