Sojojin Mali sun kwace iko da Kidal, wani muhimmin gari da ke Arewacin kasar, wanda ‘yan tawayen suka rike tsawon shekara goma.
Garin Kidal dai ta kasance muhimmiyar tunga, musamman ma ga ‘yan tawayen Tuareg da suka kasance cikin tsakiyar rikicin siyasa da kuma rashin tsaro da aka dauki tsawon lokaci ana fama da shi.
- Gimbiya Sirindhorn Ta Thailand:Shawarar “Ziri Daya Da Hanya Daya” Ta Inganta Hadin Gwiwar Al’ummun Kasa Da Kasa
- Man Da Nijeriya Ke Hakowa Ya Karu Zuwa Ganga Miliyan 1.35
Sojojin, wadanda aka ruwaito cewa suna samun goyon baya daga sojojin hayar Rasha na Wagner, sun dauki tsawon kwanaki uku suna artabu da ‘yan tawayen da nufin kwato garin.
Shugaban gwamnatin mulkin sojin kasar, Kanal Assimi Goita, ya ce ba su kammala aikinsu ba.
Ya wallafa wani sako a shafinsa na D, inda yake cewa zimmarsa shi ne ganin dukkan suna iko da dukkan yankunan kasar.
Sojojin sun bukaci fararen hula a garin Kidal da su kwantar da hankulansu.
Gwamnatin tarayya a Mali ta rasa iko da yawancin Arewacin kasar sama da shekara goma da suka wuce bayan da ‘yan tawayen Tuareg suka nemi a ba su kasarsu.
Bangaren tsaron kasar ya kara tabarbarewa ne da ayyukan masu ikirarin jihadi.
Hakan ya janyo samun juyin mulki har guda uku tun 2012.