Mulkin mallaka wata hanya ce ta tafiyar da gwamnati inda Turawan Ingila suka yi amfani da Sarakunan gargajiya wajen tafiyar da harkokin mulkinsu a yammacin Afirka. Shugaban ko jagoran al’amarin mulkin mallaka a yammacin Afirka shi ne Lord Frederick Lugard a shekarar1906.Ya fara gwada tafiyar da tsarin mulkin ne a Arewacin Nijeriya lokacin da aka ga abin an samu nasara,sai aka fara amfani da shi a sauran sassan kasashen yammacin Afirka.
An amince da Sarakunan gargajiya
Sarakuna wadanda sune ke lura da al’amuran da suka shafi al’umma a Arewacin Nijeriya al’umma suka nada su,don haka aka amince da sub a tare da wata matsala ba.Sune suka jagoranci hukumomin da ake tafiyar da al’amuran da suka shafi al’umma da ake kiran su da suna Natibe Authority. Shi ya sa babu wata matsala idan Sarakuna suka bayar da umarnin daya zo daga wurin jami’an Turawa na yin wani abu,hakan ta kasance ne saboda al’umma sun saba da samun umarni na wani abu daga wurin Sarakunan.
Sarakunan gargajiya ba su wasa da ba da umarni
Lokacin da gwamna Lord Lugard ya aiwatar da mulkin mallaka na Turawan Ingila a Arewacin Nijeriya,tun kafin lokacin da akwai hanyar da ake tafiyar da sarautar gargajiya ta tafiyar da al’umma.Sarakunan ko Sultan tuni akwai wuraren da suke karkashinsu suna mulkarsu ba tare da matsala ba,mutane kuma sun saba da al’amarin. Shi yasa mulkin ba a samu wata matsalar tafiyar da shi ba wanda yake da alaka da siyasa.
Al’amarin Haraji
Al’ummar Arewacin Nijeriya sun saba da al’amarin daya shafi Haraji saboda kuwa Talakawa sun saba da biyan Haraji nau’oi daban daban da suka hada da Jangali na dabbobi da wadanda mutane suke biya,shi yasa ba a samu wata matsala ba domin al’ummar Arewa sun saba da biyan su nau’oin harajin,domin an samu yin gyara ne lokacin da aka bullo da shi lokacin da aka fara tafiyar da mulkin mallaka a Arewacin Nijeriya.
Rashin Masu Ilmin Zamani A Arewa
A Arewacin Nijeriya bamasu ilimin zamani a lokacin kamar yadda ake da su a Kudancin Nijeriya,saboda a lokacin a Arewacin Nijeriya akwai lauyoyi wadanda suka samu horo a Ingila da kuma ‘yan jarida,alal misali a Arewacin Nijeriya ba irin wadancan mutanen wadanda Turawan mulkin mallaka za su samu matsalar tunkararsu,ba kamar a Kudancin Nijeriya ba.
Kotunan shariar musulunci
Mulkin mallaka na turawan Ingila ya samu nasara ne a Arewacin Nijeriya saboda dam tuni ana da tsarin shari’a karamar hukumar gargajiya da ake kira Natibe Authority a lokacin.Sarakuna a Arewacin Nijeriya suna da kotu inda ake shari’ar wadanda suka aikata laifi idan kuma aka samu mutum da aikata laifi ana iya yanke ma shi hukunci, wannan tsarin ne Lord Lugard ya amince da shi da yi ma shi gyara.Misali kotunan musulunci ba za su zartar da hukunci kisa ba, ba tare da amincewar jami’an Turawan mulkin mallaka da suke zaune a Larduna daban- daban a Nijeriya.
Umarnin Jami’an Ingila
Kasancewar jami’an Turawan Ingila a Arewacin Nijeriya inda suke kulawa da Larduna ana kiransu da sunan Rasdan sune suke ba Sarakunan gargajiya shawarwari, wanda hakan ne ya basu dama ta samun nasara a tafiyar da mulkinsu a Arewacin Nijeriya.Kwamishinonin Larduna su suka rika ba Sarakunan gargajiya a Arewa shawarar da ta tabbatar da mulkin Turawan Ingila ya samu nasara a yammacin Afirka.daudawa