Matashin dan wasa Nathan Tella ya ce burinsa zai cika yayin da yake shirin buga wa Nijeriya wasa a gasar neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya ta FIFA ta 2026 a wannan makon.
An sanya sunan dan wasan, mai shekara 24 da haihuwa, wanda ke wasa a kungiyar Bayer Leberkusen, cikin tawagar Super Eagles ta Nijeriya da za ta kara da Lesotho da kuma Zimbabwe.
- CGTN Ya Gabatar Da Shiri Kan Ganawar Shugabannin Sin Da Amurka
- Ganawar San Francisco: Tsaraba Daga Jawabin Shugaba Xi Kan Bukatar Sin Da Amurka Su Nuna Su Manya Ne A Aikace
An haife shi a Lambeth, da ke kasar Ingila, amma ya cancanci buga wa Nijeriya ta dalilin iyayensa, makomarsa ta kasa da kasa ta kasance batu mai mahimmanci tun lokacin da ya fara yin tasiri a bangaren matasa a Arsenal.
Tella ya shaida wa manema labarai cewa, a kullum batunsa wakiltar Nijeriya ne saboda iyalinsa za su kasance cikin matukar farin ciki domin ganin ya cika wannan burin.
“Ina alfahari da asalina na dan Birtaniya da Nijeriya kuma na yi sa’a da samun al’adu biyu, tabbas mun hada al’adun bangarorin biyu, amma gidanmu cikkaken gidan ‘yan Nijeriya ne ta fannin abinci, da al’adu” in ji dan wasan.
Tella ya kasance daya daga cikin fitattun ‘yan wasan kungiyar Burnley a kakar wasan da ta gabata yayin da kungiyar ta samu gurbin komawa matakin gasar Firimiya, amma ya koma asalin kungiyarsa ta Southampton a karshen kakar wasan.
Dan wasan gaban, wanda zai iya buga wasa a gefe ko kuma ta tsakiya, ya bayar da gudunmawar kwallaye 22 a kakar wasan da ta gabata kuma ya koma Leberkusen a kan farashin fam miliyan 20 a watan Agusta.
Sabuwar kungiyarsa ba ta yi rashin nasara ba a gasar Bundesliga na Jamus bayan wasanni 10 kuma ana tunanin bajintarsa za ta kara wa tawagar Super Eagles karfi a bangaren ‘yan wasan gaba.
Bayan rashin halartar gasar cin kofin duniya da za a yi a Katar a shekarar 2022, ‘yan Afirkan ta Yamman sun fara yakin neman gurbin shiga gasar ta 2026 inda za su fafata da Lesotho da Zimbabwe a ranakun 16 da 19 ga watan Nuwamba.
Ana sa ran Nijeriya za ta tsallake daga rukunin C a saman takwarorinta na Afirka ta Kudu da Benin, inda kasashen da suka yi nasara a rukunin za su tabbatar da samun gurbi a gasar da za a yi a kasashen Canada da Medico da kuma Amurka bayan da aka kara yawan kasashe daga 32 zuwa 48.
Tawagar Nijeriya a wasannin watan Nuwamba da aka gayyata.
Masu tsaron raga: Francis Uzoho (Omonia Nicosia, Cyprus), Olorunleke Ojo
(Enyimba), Maduka Okoye (Udinese, Italy).
‘Yan wasan baya: Ola Aina (Nottingham Forest, England), Chidozie Awaziem
(Boabista, Portugal), Bright Osayi-Samuel (Fenerbahce, Turkey), Bruno Onyemaechi (Boabista, Portugal), Kenneth Omeruo (Kasimpasa, Turkey), Semi Ajayi (West Bromwich Albion, England), Calbin Bassey (Fulham, England), Jamilu Collins (Cardiff, Wales).
‘Yan wasan tsakiya: Raphael Onyedika (Club Bruges, Belgium), Joe Aribo
(Southampton, England), Frank Onyeka (Brentford, England), Aled Iwobi (Fulham, England).
‘Yan wsan gaba: Kelechi Iheanacho (Leicester City, England), Sadik Umar (Real Sociedad, Spain), Moses Simon (Nantes, France), Ademola Lookman (Atalanta, Italy), Nathan Tella (Bayer Leberkusen, Germany), Taiwo Awoniyi (Nottingham Forest, England), Terem Moffi (Nice, France), Bictor Boniface (Bayer Leberkusen, Germany).