Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Argungu/Augie ta jihar Kebbi a majalisar tarayya, Sani Yakubu Noma ya bayyana cewa, ya kammala shirye-shiryen aurar da ‘ya’ya mata marayu 100.
Da yake zantawa da manema labarai a mahaifarsa da ke yankin Argungu a jihar Kebbi, dan majalisar ya ce, shirin auren na daya daga cikin gudunmawar da yake bayarwa wajen kyautata rayuwar marayu a mazabarsa.
- Majalisar Dokokin Kaduna Ta Dakatar Da Kansiloli 8, Ta Karɓe Ragamar Majalisar Kagarko
- Ruɗani A Kan Shari’ar Abba Da Gawuna: Kotu Ta Tabbatar Da Nasarar NNPP A Rubuce
Ya ce, za a daura auren ne a fadar mai martaba Sarkin Argungu, Alhaji Sama’ila Muhammad Mera a ranar Asabar.
“An kafa kwamiti don samun nasarar aiwatar da taron. Wadanda aka zaba domin a daura musu auren sun fito ne daga kananan hukumomi biyu da nake wakilta a Majalisar Dokoki ta kasa.
“Tuni, na sayi gadaje, katifu, kayan daki masu mahimmanci da sauran kayayyakin aure ga wadanda suka ci gajiyar shirin,” in ji shi.