Akwai alamun dake nuni da yiwuwar fuskantar karancin motocin ‘Beljium’ da ake shigowa da su daga kasashen waje wadanda kuma ake kira da ‘tokunbo’ saboda matsalolin da dillalai masu shigo da motoci suke fuskanta na karin kudaden haraji da sauran kudaden da suke biya na ka’ida kafin su shigo da motocin.
Wasu dillalan motoci da suka tattauna da manema labarai a Leagas sun ce, karyewar darajar naira da yadda dala ke hauhawa ya shafi kudaden harajin da suke biya ya kuma taimaka wajen karancin motocin da ake shigowa da su.
- Dan Majalisa Zai Aurar Da Mata Marayu 100 A Kebbi
- Sin Ta Yi Maraba Da Yarjejeniyar Tsagaita Wuta Na Wucin Gadi Tsakanin Palasdinu Da Isra’ilaÂ
Sakataren kungiyar na Jihar Legas, Mista Olaniran Adelana, ya ce, yana da matukar wahala a sayar da mota a halin yanzu sannan kuma sayo sabbin motocin yama fi wahala.
Adelana ya kara da cewa, dillalan motoci da dama sun bar sana’ar saboda matsalolin da ake fuskanta a halin yanzu, ya ce, farfadowar da naira ta yi a ‘yan kwanakin nan bai taka kara ya karya ba.
Wani dillalin motoci mai suna Mista Chinonso Amaraiwu, ya ce, duk da sayar da motoci ya dan farfado, amma rikicin a nan shi ne yadda za a dawo da wadanda aka sayar, shi ne matsalar.