Masana na ci gaba da fashin baki kan taron kolin da aka gudanar ka bunkasa tattalin arziki a tsakanin Afirka da Saudiyya da kuma Jamus.
A makon jiya ne aka gudanar da na Saudiyya, yayin da na Jamus kuma ya gudana a wannan makon.
- Kano: Kotun Daukaka Kara Ta Bukace Lauyoyin Su Mayar Da Kwafin Takardun Shari’ar
- Zaben Kano: ‘Yansanda Da Masu Zanga-zanga Sun Yi Arangama A Kano
LEADERSHIP Hausa ta tattauna da Kwamared Sabo Muhammad, wani mai sharhin lamuran yau da kullum da ke jihar Bauchi kan alfanun wannan taron, inda ya yi bayani kan taron Saudiyya.
A cewarsa, “Shugaba Bola Ahmed Tinubu irin wannan damar yake bukata domin jawo kasashe masu arziki kamar Saudiyya su zo su sanya hannun jari a musamman bangaren man fetur da iskar gas da sauransu. Na biyu kuma taron zai kara inganta kasuwanci da Saudiyya da sauran kasashen Labarawa. Abu na uku kuma shi ne domin ya tabbatar wa Saudiyya da sauran kasashe da suke da zimmar zuba jari, cewa yanzu ‘Njeriya’ wata kasa ce sabuwa wadda kofarta take a bude da ake kira ‘Free Market economy’ cewa za ka zo ka yi kasuwancinka cikin sauki kuma idan ka sanya hannun jarinka za ka samu riba mai inganci sannan babu wasu tarnake-tarnake da ake da su a baya, misali na idan ka sanya kudi babu wata wahala za ka fitar da kudinka kasar waje kamar yadda muka gani a baya. Manya-manyan kamfanoni na jiragen sama sun daina hulda da Nijeriya kamar British Airways da kuma kamfanonin da suke Daular Larabawa da kasashe da dama saboda ba su iya samun kudadensu na waje da ake biya ta dalar Amurka.
“A wannan ziyarar na shugaban kasa ya tattauna da Yarima mai jiran gado Bin Salman har ma Saudiyya ta ke da zimmar cewa nan ba da jimawa ba za ta sanya kusan dalar Amurka miliyan dari biyar shi ne kimanin riyal din Saudiyya miliyan dubu biyu a matatun man fetur na Nijeriya wanda gwamnati take da su guda hudu kuma za su sanya hannun a kan yarjejeniyar yadda za a karfafa alakar na sauran fannoni da suka shafi makamashi ta yadda za a karfafa wa kan yadda ake tafiyar da harkokin makamashi na zamani kuma shi ministan tattalin arziki na kasar Saudiyya ya ce nan da karshen wannan shekarar ko a zangon farko na shekarar da za mu shiga za a zo a yi jarjejeniya a sanya hannu.”
A cewar masanin, Bola Tinubu na kokari ne don tabbatar wa kasashen da yake ziyarta cewa, gwamnatin Nijeriya a karkashinsa tana bi dukkanin dokoki na kasuwanci na kasa da kasa kamar misalign shawarar da ya bi ta cire tallafin mai da kudin da ake narkawa wajen kare darajar Naira.
“Sannan na uku kuma, tunin a kan haraji an riga an yi kwamiti mai karfi wanda zai cire dukkanin wata sarkakiya na na haraji daban-daban da suke sanya wa kamfanoni masu hannun jarida. Da kuma bukatar da shi shugaban kasa ya ke da ita cewa su yi aiki da kasashen duniya musamman ita Saudiyya da sauran kasashen duniya musamman na Labarawa domin a samu a yaki matsalar tsaro ta yadda shi shugaba Tinubu ke son Nijeriya da Saudiyya su yi aiki tare domin yaki da akidun kungiyoyi irin su Boko Haram, ISWAP da sauransu da ke Nijeriya da yankin Chadi.”
“Abu na uku idan suka yi aiki tare a bangaren tsaro akwai akwai yiwuwar ita kasar Saudiyya za ta fi bai wa Nijeriya taimako na kayan aiki da kuma na kudade da canza bayanai na sirri tun da akwai ISIS a Nijeriya kuma ISIS suna da karfi a kasashen Labarawa ka ga Nijeriya za ta samu bayanan sirri daga wajen Saudiyya domin dakile kungiyon ISIS-ISWAP da sauran kungiyoyin ta’addanci, shi ya sanya ma a ziyarar akwai mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribado da shugaban tattara bayanai na sirri Malam Abbakar, to dukka wadannan alkairi ne, amma gaskiya ba za a ga wadannan alkairan a yanzu-yanzu ba.” Ya bayyana.