Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ya yaba da hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke na tabbatar da hukuncin da kotun sauraron kararrakin zabe ta jihar Kaduna ta yanke na tabbatar da nasarar da ya samu a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Kaduna da ya gudana a watan Maris, 2023.
Gwamnan ya kuma yabawa kotun da ta yi watsi da karar da aka shigar wacce ke kalubalantar nasararsa. “wannan shaida ce ta karfin cibiyoyin shari’armu, nasara ce kuma ga dimokuradiyya da kuma tabbatar da ra’ayin mutane.”
- Majalisar Dokokin Kaduna Ta Dakatar Da Kansiloli 8, Ta Karɓe Ragamar Majalisar Kagarko
- Sojoji Sun Kashe ‘Yan Ta’adda 5, Sun Kwato Makamai A Kaduna
Hakan na kunshe ne acikin wata sanarwa da Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamnan Jihar Kaduna, Muhammad Lawal Shehu ya fitar ga manema labarai jim kadan bayan bayyana hukuncin kotun da ta tabbatar da Nasarar Gwamna Uba Sani a matsayin halastaccen gwamnan jihar a ranar 24 ga watan Nuwamba, 2023.
A yayin da yake nuna farin ciki da jin dadinsa bisa tabbatar da nasararsa da kotun daukaka kara ta yi, Gwamna Uba Sani ya bukaci sauran jam’iyyun adawa da su hada hannu don ciyar da jihar Kaduna gaba.
Gwamna Uba Sani da Mataimakiyarsa, Dr. Hadiza Sabuwa Balarabe, suna mika godiya ga duk ‘ya’yan jam’iyyar APC, da kuma jama’ar jihar Kaduna bisa irin goyon bayan da suka bayar.
Ina kira ga ’yan uwana ‘yan sauran jam’iyyar hamayya da su amince da wannan hukuncin bisa gaskiya da kuma cewa, shi ne ra’ayin al’umma. Lokaci ya yi da za mu hada kai don ciyar da babbar jiharmu gaba.” inji Gwamna Sani