Dakarun da ke kula da wanzar da zaman lafiya a Jihar Filato sun bayyana cewa, rundunar soji ta musamman ta yi nasarar kashe ‘yan bindiga 7 tare da cafke wasu 33 a wasu hare-hare daban-daban a fadin jihar da ma wasu sassan Jihar Kaduna.
Kakakin Rundunar Sojin, Kyaftin Oya James ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar.
- An Gudanar Da Bikin Reel Africa A Birnin Shanghai
- Labarin Ƙarya: Babu Inda Gwamna Dauda Lawal Ya Kashe Naira Miliyan 400 Don Tafiye-tafiye
James ya ce sojojin sun kuma ceto mutum 15 da aka yi garkuwa da su tare da dakile hare-haren da aka kai a wasu yankuna uku masu rauni a cikin wannan lokacin.
A cewarsa, a ranar 13 ga watan Nuwamba, 2023, sojojin da ke aikin gano bakin zaren, sun kama Mista Suleiman Mohammed da bindiga kirar AK 47 daya da wayar hannu, a yankin Bakin Kogi, Karamar Hukumar Zangon Kataf ta Jihar Kaduna.
James ya kuma ce sojoji, a ranar 13 ga watan Nuwamba, 2023, sun kama wasu mutane biyar da ake zargi da kai hari kan Mista Sati Pewat a gonarsa da ke Kauyen Tileng Paat a Karamar Hukumar Mangu ta Jihar Filato.
Ya kara da cewa, a ranar 14 ga watan Nuwamba, 2023, sojoji sun gudanar da wani sumame a Kauyen Tileng Paat da ke gundumar Pushit a Karamar Hukumar Mangu, jihar Filato, inda suka kama mutum daya Umurana Adamu dauke da bindiga kirar AK 47, da kwanso daya, da harsashi 9 na musamman na 7.62mm na musamman. .
“Hakazalika, a ranar 14 ga Nuwamba, 2023, sojojin da ke aiki da sahihan bayanai sun kama wani da ake zargin dillalin makamai ne, Mista Rufa’i Abdullahi a yankin Kamuru a Karamar Hukumar Zangon Kataf ta Jihar Kaduna.