Rundunar Shiyyar Kaduna ta hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, ta tabbatar da samun hukuncin dauri ga wani Jesse Kassah, (mai suna Debaun Smith Wayne).
An yanke masa hukuncin daurin shekara biyu a gidan yari.
- Shugaban Africa CDC Ya Yaba Da Hadin Gwiwar Sin Da Afrika A Bangaren Kiwon Lafiyar Al’umma
- Za A Fuskanci Karancin Motoci A Nijeriya Sakamakon Karin Haraji
An samu Kassah da laifin yin kwaikwayon wani sojan Amurka kuma ya sayar da tikiti a Facebook ga wani Caitlin Morgan.
Kamar yadda bincike ya nuna, Kassah ya yi amfani da sunansa wajen damfarar wadanda abin ya shafa a cikin lamarin.
Mai shari’a Darius Khobo na babbar kotun Jihar Kaduna, Kaduna ne ya daure shi a gidan yari, bayan da ya amsa laifin da ake tuhumarsa da aikatawa a gaban kotu yayin da hukumar EFCC ta gurfanar da shi a gaban kuliya.
An bayyana hakan ne ta hannun hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa a cikin wani sakon da ta wallafa a shafinta na D (tsohuwar Twitter).
Sanarwar ta kara da cewa, “Kai Jesse Joshua Kassah (aka Debaun Smith Wayne), (M) tsakanin watan Janairu zuwa Oktoba 2023 a Kaduna da ke karkashin ikon wannan kotun mai daraja, ka aikata laifi, kamar haka; karya ya gabatar da kanka a matsayin Debaun Smith Wayne; Wani jami’in sojan Amurka kuma mai sayar da tikiti a Facebook (wani shafin kafar yada labarun kan layi) ga wani Caitlin Morgan kuma wanda ya nuna cewa kun san karya ne sannan ka aikata laifin da ya saba wa doka kuma hukuncin da za a yi maka ya dace a karkashin sashe na 142 (1) na dokar Penal Code na Jihar Kaduna, na shekarar 2017″.
Ya amsa laifin da ake tuhumarsa da shi lokacin da aka karanta masa.
Da yake gabatar da rokonsa, lauyan masu shigar da kara, M. Arumemi, ya bukaci kotun da ta yanke wa wanda ake kara hukunci kamar haka.
Alkalin “ya yanke wa Kassah hukuncin daurin shekaru biyu a gidan yari tare da zabin tarar Naira 150,000.00.
Alkalin ya kuma bayar da umarnin a kwace wayar Samsung Galady A02 da aka yi amfani da ita wajen aikata laifin tare da mika ta ga Gwamnatin Tarayyar Nijeriya.
Sanarwar ta kara da cewa, “Wannan shi ne karo na farko da Kassah zai tafi gidan gyaran hali a lokacin da aka kama shi a unguwar Karji da ke Kaduna bisa laifukan da suka shafi intanet.”