Wakilin dindindin na kasar Sin a hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya (IAEA) Li Song, ya yi kira ga kasa da kasa a hukumar, da su tattauna domin shawo kan barazanar yaduwar makaman nukiliyar da yarjejeniyar AUKUS ta sayen jiragen karkashin ruwa na yaki masu amfani da makamashin nukiliya ke yi.
Li Song ya fadawa wani taron kwamitin gwamnoni na hukumar IAEA cewa, yarjejeniyar AUKUS wadda aka kulla tsakanin Amurka da Birtaniya da Australia, domin sayarwa Australia jiragen karkashin ruwa na yaki masu amfani da makamashin nukiliya, na da mummunan tasiri kan tsaron duniya da ma yankin Asia da tekun Pasific. Haka kuma kalubale ne ga yarjejeniyar kasa da kasa kan hana yaduwar makaman nukiliya da tsarin tsaron nukiliya na hukumar IAEA.
- Kasar Sin Ta Bukaci Japan Ta Amince Kasashen Duniya Su Sa Ido Kan Yadda Take Zubar Da Ruwan Dagwalon Nukiliya Cikin Teku
- Shugaban Africa CDC Ya Yaba Da Hadin Gwiwar Sin Da Afrika A Bangaren Kiwon Lafiyar Al’umma
Ya ce, irin wannan hadin gwiwa ya sabawa manufofin yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya ta NPT, haka kuma wani nau’i ne na nuna fuska biyu.
Li Song ya kara da bayyana cewa, yarjejeniyar wadda ta kunshin batutuwa na siyasa da tsaro da shari’a da ma’aikata, za ta haifar da wani muhimmin yanayi, haka kuma za ta yi mummunan tasiri kan ingantawa da daukaka tsare-tsaren tsaro na hukumar IAEA da sauran tsare-tsare masu ruwa da tsaki.
Bugu da kari, wakilin na Sin ya ce, dukkan wadannan manyan batutuwa ne da ya kamata kasashe mambobin hukumar su dauka da muhimmanci, kana su yi nazari mai zurfi da kansu domin tafiyar da su yadda ya kamata. (Fa’iza Mustapha)