Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ya kaddamar da aikin gina birnin koyar da sana’o’i da fasaha a Rigachikun da ke karamar hukumar Igabi a jihar.
Ya ce, idan aka kammala cibiyar, za ta horas da matasa 400 duk bayan wata Uku-uku, a duk Shekara, za a horas da matasa 1,600 sana’o’i 19 daban-daban.
- ‘Mutuwar Aminu S. Bono Ta Girgiza Kannywood’
- Firaministan Kasar Sin Ya Gana Da Ministar Harkokin Wajen Faransa
Da yake jawabi yayin kaddamar da ginin a ranar Asabar, Gwamnan ya ce za a sake gina irin birnin a duk fadin mazabun sanatoci uku na tarayya da ke jihar.
Gwamna Uba ya bayyana cewa, wannan kuduri na daga cikin tsarin gwamnatin tarayya na cike gibin da ake da shi a bangaren fasaha da koyar da sana’o’i a tsakanin matasa wanda gwamnatin ta himmatu wajen habbakawa daga kashi 23 zuwa 46 cikin 100 nan da shekarar 2030.
A cewarsa, “A lokacin yakin neman zabenmu, mun yi wa al’ummar jihar Kaduna alkawarin bunkasa ci gaban al’umma domin baiwa matasanmu ilimin fasaha da za su yi gogayya da takwarorinsu na duniya. Da yawan ayyukan da ya dace a baiwa mutanenmu na cikin gida amma sai a mikawa baƙi saboda ƙarancin fasaha. Don haka, mun gano akwai bukatar gaggawa na a sake horas da mutanenmu fasahohi da kirkire-kirkire don su zama abin nema wajen daukar ayyuka.
“Wannan birnin kimiyya da fasaha na Jihar Kaduna da za a gina, za a horas da matasa a fanni daban-daban da ya hada da:
- Takardar shaidar kwarewa a fannin Kwamfuta na kasa da kasa daga Microsoft Cisco.
- Takardar shaidar kwarewa a fannin walda a bangaren man fetur da gas
- Takardar shaidar kwarewa a fannin aikin tukin mota.
- Takardar shaidar kwarewa a fannin firiji da na’urar sanyi (AC)
- Takardar shaidar kwarewa a fannin wutar lantarkin motoci.
- Takardar shaidar kwarewa a fannin gyaran motoci
- Takardar shaidar kwarewa a fannin dafa abinci
- Takardar shaidar kwarewa a fannin walda
- Takardar shaidar kwarewa a fannin aikin sanya dandamalin tayels
- Takardar shaidar kwarewa a fannin lantarki mai amfani da hasken rana.
- Takardar shaidar kwarewa a fannin aikin Aluminiyom
- Takardar shaidar kwarewa a fanni Ado Da kwalliya.
Anasa jawabin, Sakataren zartarwa na hukumar kula da ilimin fasaha ta kasa (NBTE), Farfesa Idris Bugaje wanda Darakta a hukumar NBTE, Abbati Mohammed ya wakilta ya ce, wannan shiri na da matukar amfani ga raya matasa wanda hakan zai habbaka tattalin arzikin kasa. Don haka, Gwamna Uba Sani ya cancanci a yaba masa bisa jajircewarsa na gani al’umma ta ci gaba.
Ginin Birnin zai kasance kamar haka: Dakunan horaswa 16, Dakunan kwanan dalibai guda hudu, ajujuwa, ginin gudanarwar birnin, asibiti, wurin cin abinci, kantina, filin wasan kwallon kwando, filin wasan kwallon kafa, masallaci, dakin janareta, bandakuna da filin ajiye motoci.