‘Yan watanni bayan ya karbi Addinin Musulunci wani matashi mai sunan Ibrahim ya rubuta Al-kur’ani mai girma da rubutun hannu a garin Birnin Gwari ta Jihar Kaduna.
Malaminsu Abu Anas Al-baahy ya ce, bayan ya shiga ajinsu na ‘Faslu Imamu Malik Bin Anas’ sai ya tarar da shi da Al-kur’aninsa a gefe yana ta kokarin ganin ya rubuta Al-kur’ani ta hanyar kwafa yana rubuta shi a littafi.
- Mun Damu Kan Bayyanar Mayakan Kungiyar Ansaru A Yankinmu — Mutanen Birnin Gwari
- ‘Yan Bindiga Sun Shimfida Wa Al’ummar Yankin Birnin Gwari Sharudda Noma A Daminan Bana
Malamin na su ya bayyana cewa, hakika ganin haka ya sanya shi tsaya wa cak cike da farin ciki yana kallon ikon Allah.
Shi dai wannan matashin da sunansa Ibrahim, sunan mahaifinsa Sylvester, watanni biyar baya ko harafin Alifun baya iya furtawa balantana ya rubuta, cikin ikon Allah bayan shigarsa Islamiyyar At-tatbiqul Islamiya, yau ga shi AlQur’anin ma yake kokarin ya rubuce wa duka.
Daga Abdulnasir Y. Ladan (Sarki Dan Hausa)