Ana kallon littafi mai taken “Dabarun Xi Jinping game da yadda ake tafiyar da harkokin kasa da kasa” wanda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya rubuta, a matsayin “tagar tunani” ga al’ummomin kasa da kasa, yayin da suke kokarin fahimtar harkokin kasar Sin, don haka ne ma ake kara wallafa littafin a sassan duniya da harsuna daban daban.
- Karin Kamfanoni Za Su Halarci Baje Kolin Kayayyakin Da Ake Amfani Da Su Na Kasa Da Kasa Na Kasar Sin
Masanin harshen Portugal ‘dan asalin kasar Brazil, dake aiki a kwalejin harsunan waje ta lardin Zhejiang na kasar Sin José Medeiros da Silva, ya taba shiga aikin fassara littafin, ya kuma bayyana cewa, littafin da aka wallafa da harsuna daban daban a fadin duniya, ya bude wata taga ga al’ummomin kasa da kasa, yayin da suke kokarin fahimtar tunanin gurguzu mai tsarin musamman na kasar Sin a sabon zamanin da ake ciki, da kuma manyan sakamakon da kasar Sin ta samu.
Silva ya kara da cewa, littafin da shugaba Xi ya rubuta yana cike da abubuwa da dama, wadanda ba ma kawai za su jagoranci ci gaban kasar Sin ba, har ma za su taka rawa wajen tafiyar da harkokin kasa da kasa, a lokacin da kasashen duniya suke fuskantar manyan sauye-sauyen da ba a taba ganin irinsu a cikin shekaru dari daya da suka gabata ba. Yana mai cewa,
“Musamman ma a bangaren kokarin da kasar Sin take yi, yayin shiga harkokin kasa da kasa. Alal misali, shawarar ‘ziri daya da hanya daya’ da shugaba Xi ya gabatar, da tunanin ‘gina kyakkyawar makomar bil adam ta bai daya’, dukkansu sun burge ni matuka, saboda duk wadannan sun nuna cewa, dabarun kasar Sin suna ba da babbar gudummowa, ga kafa sabon tsarin kasa da kasa.” (Mai fassarawa: Jamila daga CMG Hausa)