Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya bukaci Shugaba Tinubu da ya sanya wa ministocinsa takunkumin tafiye-tafiye zuwa kasashen ketare lokacin da ake kare kasafin kudin ma’aikatu.
Akpabio ya ce irin wadannan tafiye-tafiye na hana ministocin da shugabannin hukumomin gwamnati bayyana a gaban ‘yan majalisu domin kare kasafin kudin da suka gabatar da kuma tuhumar da majalisa ke yi a kan wasu ayyukan da ake sakawa.
- Ya Dace Kasashen Da Suka Ci Gaba Su Cika Alkawuran Da Suka Yi Game Da Sauyin Yanayi
- An Kammala Aikin Bututun Karkashin Ruwa Na Sabuwar Hanyar Sin Da Ta Ratsa Teku
Shugaban majalisar ya yi alkawarin cewar za su bincike kasafin da Shugaba Tinubu ya gabatar kamar yadda kundin tsarin mulki ya ba su dama, kafin amincewa da shi.
Akpabio ya kuma bukaci bangaren zartarwar da ya nemo hanyar rage basussukan da ake bin Nijeriya, duk da yake sun san cewar wannan gwamnati ta gaji wasu basussukan daga gwamnatin baya.
Shugaban majalisar ya yi kuma alkawarin hada kai da hukumomin yaki da cin hanci da rashawa domin dakile hanyoyin da jami’an gwamnati ke amfani da su suna karkata dukiyar jama’a.
Wannan shi ne kasafin kudi na farko da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gabatar tun bayan hawan sa mulki a ranar 29 ga watan Mayu 2023.