Tsohon sakataren harkokin wajen Amurka Henry Kissinger ya rasu.
Ya rasu yana da shekaru 100 a duniya.
- Kwace Wa NNPP Zaben Kano Na Iya Haddasa Tashin Hankali A Afrika – NNPP
- Gwamnatin Kaduna Ta Kaddamar Da Kwamitin Mutum 8 Don Inganta Harkokin Aikin Hajjin 2024
Kissinger ya yi aiki a matsayin babban jami’in diflomasiyyar Amurka kuma mai ba da shawara kan harkokin tsaro a lokacin gwamnatin Nixon da Ford.
Ya yi aiki a matsayin mai bada shawara kan harkokin tsaro da sakatariyar harkokin waje kasar, ya mutu a ranar Laraba yana da shekaru 100, in ji kamfanin dillancin labarai na Reuters.
Ya mutu ne a gidansa da ke Connecticut, a cewar wata sanarwa.
Ya yi aiki da kwamitin Majalisar Dattawan kasar game da barazanar nukiliyar Koriya ta Arewa.
A watan Yulin shekarar 2023 ya kai ziyarar ba-zata a birnin Beijing domin ganawa da shugaban kasar Sin Xi Jinping.
Tuni shugabannin duniya suka shiga aike wa Amurka ta’aziyyar rasuwar Kissinger.