Kamar yadda ya faru a manyan zabukan da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabarairu da ranar 18 ga watan Maris 2023, a zaben kujerar gwamna da aka yi kwanan nan a Jihohin Kogi da Imo da Bayelsa ma an tafka rikice-rikice har ya kai ga rasa rayuka. An kuma samu rahotannin saye da sayarwar kuri’u, sace-sacen akwatin zabe da kuma wasu rahotannin na arcewa da na’urar zabe ta BBAS.
Kamar yadda aka zata, korafe-korafen da ke tafiya kotun sauraron kararrakin zabe sai karuwa suke yi amma kuma wadanda suka aikata laifukan zaben suna yawo a tituna abin su, ba tare da an gurfanar da su a gaban kuliya ba. Sakamakon zabukan da aka yi ya gamu da shakku sannan INEC na fuskantar rasa kima da mutuncinta a idanun ‘yan kasa, a daidai lokacin da ake kara kira na a tabbatar da hukunci a kan masu aikata laifukan zabe.
- Sin Ta Fitar Da Takardar Bayani Game Da Dabarun Warware Rikicin Isra’ila Da Falasdinawa
- Al’ummun Amurka Sun Yi Kira Ga Kyautata Dangantaka Tsakanin Sin Da Amurka
Duk da ya kamata a lura cewa, an gabatar da wasu sauye-sauye a dokokin zabe bisa yadda aka bukata bayan zaben shekarar 2019 kamar yadda ake iya gani a dokar zabe ta shekarar 2022, amma sarkakiyar da ake ganin ta sarke zabuka da sakamakonsu a Nijeriya su ne yadda masu aikata laifukan zabe ke cin karensu ba babbaka da kuma rashin hukunta su.
Bayan kammala zaben shugaban kasa da na majalisun kasa na ranar 25 ga Fabarairu, nan take shugaban rundunar ‘yansanda na lokacin, Usman Baba, a taron da ya yi da manyan hafsoshin rundunar a Abuja, ya bayyana cewa, rundunar ta samu nasarar kai dauki a korafe-korafen zabe 185, sun kuma kama masu aikata laifukan zabe har mutum 203 tare da kama makamai 18.
“Haka kuma an kama masu laifukan zabe 304 a yayin zabukan gwamna da na ‘yan majalisun jihohi da aka cafke masu aikata laifuka 578 da makamai 48.
“Wannan ya hada da masu laifi 161 a Jihar Kano, 45 a Jihar Legas, 49 a Jihar Sakkwato, 16 a Jihar Kuros Ribas, 22 a Jihar Jigawa, 17 a Jihar Nasarawa da kuma mutum 18 a Jihar Oyo, da sauransu”.
Ya kuma bayyana cewa, rudunar ta ci gaba da bincike a kan laifukan a sashin kula laifukan zabe, inda aka ce za a aika su sashin shari’a na hukumar zabe daga nan ne za su gabatar da su a gaban kotu don hukutansu.
Tsohon shugaban rundunar ‘yansanda ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa, za su hada kai da hukumar zabe don tabbatar da an hukunta dukkan wadanda aka samu da aikata laifukan zabe ba tare da bata lokaci ba don tabbatar da adalci kuma haka ya zama darasi da tsaftace tsarin dimokuradiyyar Nijeriya.”
A zabukan da aka gudanar kwanan nan, kungiyoyi masu zaman kansu da suka sa ido, da dama sun bayar da rahoton yadda masu rike da madafun iko suka yi amfani da mukamansu wajen murde zabe da yadda ‘yansiyasa suka yi ta saye da sayar da kuri’u da kuma yadda wasu hukumomi kamar INEC, jam’iyyun siyasa da rundunonin tsaro suka kasa yin aikin su yadda ya kamata a daidai lokacin da ake tafka wadannan laifukan.
A dakin tattara bayanan yadda ake gudanar da zabukan na kungiyoyi masu zaman kansu, sun bayar da rahotannin yadda aka yi cuwa-cuwar zabe da yadda aka jirkita sakamakon zabukkan gwamna da aka yi a jihoji uku wanda a cewarsu hakan na iya jefa ayar tambaya a kan inganci da sahihancin zaben gaba daya da ma makomar tsarin dimokuradiyya a Nijeriya.
‘Yan Nijeriya sun zaci masu ruwa da staki za su dauki darasi daga zabukkan da aka yi a baya, musamman an sa rai INEC za ta kara inganta ayyukanta a zabukan da aka yi kwanan nan amma hakan bai yiwu ba don zabukan ma sun zama abin takaici.
Zabukan gwamna da aka yi a wadannan jihohin tamkar wani babban koma baya ne ga tsarin dimokurudiyya a Nijeriya.
Tun da aka fara jumhuriyya ta biyu a shekarar 1999, duk wani zabe da aka yi ya fuskanci matsaloli na laifukan zabe da dama.
Zabukan da suka biyo baya a tarayya, jihohi da kananan hukumomi sun fuskanci matsaloli da dama inda ‘yansiyasa ke rungumar tashin hankali don biyan bukatunsu.
Tabbas laifukan zabe sun kasance babbar barazana ga gabatar da sahihin zabe a Nijeriya musamman ganin suna kaiwa ga tayar hankali da kasshe-kashe a wasu lokuta.
Yayin da wasu masu lura da al’amuran yau da kullum suke da ra’ayin cewa tsarin shari’armu ne ke da rauni, wasu kuma na ganin ba zai yiwu a ce INEC, a matsayinta ta mai gudanar da zabe ta zama wadda za ta gurfanar tare da hukunta masu laifukan zabe ba.
A wata mukala da ya gabatar a zauren ‘Chatham House’ da ke Landan, shugaban INEC, Farfesa Yakubu Mahmoud ya bayyana yadda hukumar ta gaza wajen hukunta masu laifukan zabe.
Ya ce: “Duk da doka dokar zabe ta ba hukuma ikon hukunta masu laifukan zabe, amma hukumar ba ta da karfi da kayan aikin kamawa tare da gudanar da bincike yadda kamata don tabbatar da hukunta masu aikata laifukan zabe.”
“A kan haka INEC take goyon bayan kafa Hukumar Hukunta masu laifukan Zabe da kotun musamman ta hukunta masu laifukan zabe, kamar yadda wasu kwamitocin da gwamnatin tarayya ta kafa suka bayar da shawara, musamman kwamitin Uwais na shekarar 2009, da kwamitin Lemu na shekarar 2011 da kuma kwanitin Nnamani na shakarar 2017.”
A bara, wannan jaridar ta nemi majalisar kasa ta gagguta zartar da dokar laifukan zabe ta shekarar 2021 don tsohon shugaban kasa Buhari ya sanya hannu.
Da an sanya wa dokar hannu da ta karfafi hukumar zabe wajen gudanar da binciken masu laifukan zabe tare da hukunta su, dokar ta kuma yi tanadin daurin shekara 20 ga duk wanda aka samu da laifin sace akwatin zabe a yayin da ake gudanar da zabe.
A ra’ayinmu, ba zai yiwu Nijeriya ta ci gaba da jiran majalisar kasa a kan zartar da dokar laifukan zaben ba musamman ganin kamar majalisar ba ta da sha’awa a kan dokar, kuma ga shi wadanda suka aikata laifukan zaben na yawatawa ba tare da an hukunta su ba.