• English
  • Business News
Friday, October 24, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Dumamar Yanayi Ta Haddasa Ruwan Saman Ba-zata A Arewa – NiMet

by Bello Hamza and Yusuf Shuaibu
2 years ago
Yanayi

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Kashe ‘Yan Ta’adda 50, Sun Daƙile Hare-Hare A Borno

Harkokin Ciniki Da Zuba Jari Tsakanin Sin Da Afirka Sun Samu Ci Gaba Mafi Girma a Shekaru 5 Da Suka Gabata

Hukumar Kula da Yanayi ta Nijeriya (NiMet) ta bayyana cewa sakamakon dumamar yanayi ne ta haddasa ruwan sama a wasu sassan arewacin Nijeriya a karshen makon da ya gabata zuwa farkon makon nan.

A cewarta, wannan na kara tabbatar da irin illar da gurbacewar sararin samaniya ke haifarwa, kuma ya zama dole a hada hannun wajen rage dumamar yanayi ta hanyar rage yadda iskar ‘carbon diodide’ ke gurbata muhalli.

  • Xi Ya Bukaci A Tsagaita Bude Wuta Tare Da Gudanar Da Tattaunawar Zaman Lafiya Kan Rikicin Falasdinu Da Isra’ila
  • Al’ummun Amurka Sun Yi Kira Ga Kyautata Dangantaka Tsakanin Sin Da Amurka

Hukumar ta bayyana hakan ne a wajen wani taron kara wa juna sani da ta shirya wa ‘yan jarida tare da hadin gwiwar Majalisar Dinkin Duniy na, wajen tunatar da ‘yan jarida kan dumamar yanayi ta yadda za su fadakar da al’ummar kasar nan.

Taron ya gudana ne a Otel din Rock Biew da ke Abuja, inda ta ce wannan wani sharar fage ne kan babban taron da aka fara a kasar Dubai daga ranar 30 ga Nuwamba zuwa 12 ga Disamba.

Hukumar NiMet ta yi nemi ‘yan jarida su kara kaimin fadakar da al’ummar Nijeriya kan illar dumamar yanayi a bangaren lafiya da tattalin arziki da kuma yadda za a magance matsalolin ta hanyar da ta dace.

A cewarta, ta dauki nauyin bayar da horo ga ‘yan jarida ne kan dumamar yanayi, saboda ayyukan ‘yan jarida ba zai iya misultuwa ba wajen fadakar da al’umma illarsa da kuma hanyoyin magance lamari.

Da yake jawabi a wurin taron, wakilin Majalisar Dinkin Duniya a Nijeriya Mattias Schmale, ya ce dukkan kasashen duniya na fama da matsalar dumamar yanayi, amma kasashen da suka ci gaba sun dauki matakin rage matsalolin wanda hakan ya sa suke kokarin bayar da tallafi ga kasashe masu tasowa irinsu Nijeriya, domin a gudu tare a tsira tare.

Ya ce kididdiga ta nuna cewa kasashen Nahiyar Afirka su suka fi fuskantar barazanar kamuwa da illolin dumamar yanayi, wanda hakan  ya sa Majalisar Dinkin Duniya ta mayar da hankali wajen taimaka musu.

Wakilin ya kara da cewa a 2023, an samu sauye-sauyen canjin yanayi ba ma a Nijeriya ba har da duniya baki daya, wanda akwai bukatar hada kannu da karfe wajen taimaka wa kasashe domin a tsira daga illar lamarin.

A tattaunawarsa da manema labarai, wakilin Kungiyar Masu Kula da Yanayi ta Duniya (WMO) a yankin yammaci da Afirika ta tsakiya, Mista Biyarnada Edward Gomez, ya bayyana cewa, an shirya taron ne don zaburar da ‘yan jarida da dukkan masu ruwa da tsaki wajen tattaunawa tare da bayar da rahotannin da suka shafi dumamar yanayi da yadda take addabar al’ummar sassan duniya da kuma irin gudunmwar da kowa zai bayar don rage irin matsalolin da ake fuskanta.

Ya ce, wannan yana da muhimmanci musamman da yake ana gudanar da babban taron ne da majalisar Dinkin Duniya ta shirya a kan dumamar yanayi a Hadaddiyar Daular Larabawa, taron shi ne na 28 tun da aka fara gabatarwa duk shekara.

“Muna zama ne a kan dumamar yanayi. Ana yin zaman saboda dumamar yanayi na addabar kowa a duniya. Kowa da kowa. Daga Nijeriya zuwa nahiyar Turai da Asiya da Amurka. Kuma babban abin da yake haddasa dumamar yanayi shi sinadarin CO2 din da suke fita wanda ni da kai duk muna taimakawa wajen gurbata muhalli. Idan kana tukin mota, motarka tana shan mai. Mai kuma yana fitar da sinadarin ‘Carbon Diodide’ cikin sararin samaniya idan kana amfani da ‘Air conditioner’ shi ma yana fitar da iskar. idan ka kunna wutar lantarki shi ma yana fitar da gurbatacciyar iska. Toh dukkanmu muna taimakawa wajen fitar da shi. Amma akwai kasashen da suka fi yi fiye da wasu, kasashen da suke da manyan kamfanoni, sun fi haifar da dumamar yanayi fiye da kananan kasashe”.

Mr Gomez ya kuma kara da cewa, “Dumamar yanayi na faruwa, me za mu yi a kai? Dole mu nemo hanyoyin da za mu saba. Misali, idan ana samun ruwa sosai da yake janyo ambaliya me za mu yi? Dole mu nemo hanyar da za mu saba. Ko kuma dalilin wannan zaman shi ne domin zaburar da ‘yan jarida domin su samu karfin gwiwa da ra’ayi a kan wadannan labarun, za su iya rubuta labarai a kan abubuwan da ke faruwa kuma su taimaka wajen sabawa da kuma shirya wa manyan dumamar yanayi, kuma muna kira gare ku ‘yan jarida ku sa ra’ayinku a kai, saboda wannan zai shafe ka kuma zai shafe shi kuma zai shafe ni, ya shafi dukkan al’umma.

Ya kara da cewa, “lallai mun yi sa’a, Nijeriya ba ma cikin manyan garuruwan da illolin dumamar yanayi yake shafa, idan ka samu kanka a garin da ake ambaliya sosai za ka iya rasa rayuwarka, zan iya rasa rayuwata. Saboda haka dukkanmu ya kamata mu maida hankali a kan abin da yake tafiya kuma mu fitar da labarun da za su tsawatar wa mutane don su dauki mataki a kan lokaci. Kuma a shirye muke mu ci gaba da ba ku wasu labarai da suka shafi dumamar yanayi don watsawa ga al’ummar yankunan karkara.”

Taron ya samu halartar masana daga cibiyoyin bincike, malaman jami’o’i da ‘yan jarida daga kafafen watsa labarai na jihohin Nijeriya da babban birnin tarayya Abuja.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Sojoji Sun Kashe Mayakan Boko Haram 6, Sun Kama Wasu A Borno
Manyan Labarai

Sojoji Sun Kashe ‘Yan Ta’adda 50, Sun Daƙile Hare-Hare A Borno

October 23, 2025
Harkokin Ciniki Da Zuba Jari Tsakanin Sin Da Afirka Sun Samu Ci Gaba Mafi Girma a Shekaru 5 Da Suka Gabata
Ra'ayi Riga

Harkokin Ciniki Da Zuba Jari Tsakanin Sin Da Afirka Sun Samu Ci Gaba Mafi Girma a Shekaru 5 Da Suka Gabata

October 23, 2025
Uwargidan Tinubu Ta Ƙaddamar Da Ɗakin Karatu Na E-learning A Zamfara
Labarai

Uwargidan Tinubu Ta Ƙaddamar Da Ɗakin Karatu Na E-learning A Zamfara

October 23, 2025
Next Post
Allah Ya Girmama Annabi (SAW) Cikin Fadi Da Aikatawa

Allah Ya Girmama Annabi (SAW) Cikin Fadi Da Aikatawa

LABARAI MASU NASABA

Fahimtar Sabon Tunani: Samar Da Wadata Ga Dukkan Jama’a Ta Daidaita Gibin Dake Tsakanin Hamshakai Da Matalauta

Fahimtar Sabon Tunani: Samar Da Wadata Ga Dukkan Jama’a Ta Daidaita Gibin Dake Tsakanin Hamshakai Da Matalauta

October 23, 2025
Shugaban Senegal: Kasar Sin Ta Zama Abin Koyi Ga Kasashe Masu Tasowa

Shugaban Senegal: Kasar Sin Ta Zama Abin Koyi Ga Kasashe Masu Tasowa

October 23, 2025
Sojoji Sun Kashe Mayakan Boko Haram 6, Sun Kama Wasu A Borno

Sojoji Sun Kashe ‘Yan Ta’adda 50, Sun Daƙile Hare-Hare A Borno

October 23, 2025
Me Ake Fatan Gani A Shirin Sin Na Raya Kasa Na Shekaru Biyar Biyar Na Gaba

Me Ake Fatan Gani A Shirin Sin Na Raya Kasa Na Shekaru Biyar Biyar Na Gaba

October 23, 2025
Harkokin Ciniki Da Zuba Jari Tsakanin Sin Da Afirka Sun Samu Ci Gaba Mafi Girma a Shekaru 5 Da Suka Gabata

Harkokin Ciniki Da Zuba Jari Tsakanin Sin Da Afirka Sun Samu Ci Gaba Mafi Girma a Shekaru 5 Da Suka Gabata

October 23, 2025
Uwargidan Tinubu Ta Ƙaddamar Da Ɗakin Karatu Na E-learning A Zamfara

Uwargidan Tinubu Ta Ƙaddamar Da Ɗakin Karatu Na E-learning A Zamfara

October 23, 2025
Kungiyar IOMed Za Ta Taka Rawar Gani Wajen Gina Al’umma Mai Makomar Bai Daya 

Kasar Sin Ta Karyata Rahoto Na Zuki-ta-malle Da Wata Cibiyar Binciken Amurka Ta Fitar Game Da Hadin Gwiwar Sin Da Yammacin Afirka

October 23, 2025
An Kammala Taron JKS Inda Aka Amince Da Shawarwari Kan Shirin Ci Gaban Kasar Sin Na Shekaru Biyar-biyar Karo Na 15

An Kammala Taron JKS Inda Aka Amince Da Shawarwari Kan Shirin Ci Gaban Kasar Sin Na Shekaru Biyar-biyar Karo Na 15

October 23, 2025
Tinubu Ya Rantsar Da Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC

Tinubu Ya Rantsar Da Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC

October 23, 2025
Sanarwar Bayan Taron Jks: Mene Ne Sirrin Kwarin Gwiwar Kasar Sin?

Sanarwar Bayan Taron Jks: Mene Ne Sirrin Kwarin Gwiwar Kasar Sin?

October 23, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.