A ranar Talata, gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya ce, gwamnatinsa za ta cigaba da amfani da fahasa domin kawo karshen matsalolin da ake fuskanta a cikin gida.
A cewarsa, ta hakan, za a samu wadata jihar da abinci, saukaka harkokin sufuri, kiwon lafiya mai inganci da nagarta, hadi da samar da ilimi mai inganci hadi da sauran bangarori.
- Gwamna Uba Sani Ya Kafa Kwamitin Binciken Matsalolin Aiki Hajji
- Kamfanonin Siminti Ke Haifar Da Kashi 7 Na Dumamar Yanayi A Duniya – Dangote
Sanwo-Olu wanda ke magana yayin wani taron shekara shekara na bunkasa harkokin kasuwanci da ya gudana a Legas.
A cewarsa, gwamnatinsa na amfani da sauyin zamanin da duniya ke amfani da su, don haka za su kara sanya ido wajen nemi muhimman abubuwan da suka shafi na fasaha tare da kawosu cikin jihar domin saukaka harkokin rayuwa.
Ya ce, “Daga cikin shirye-shiryen da muke gudanarwa domin bunkasa bangaren fasaha da bunkasar tattalin arziki na’urar fiber optics da muke shimfidawa domin bunkasa harkokin yanar gizo, shirin asusun samar da ayyuka na jihar Legas, wanda ya taimaka wa masu matsakaita da kananan masana’antu sama da 12,710 domin samun rancen sama da biliyan 8.4. “Mun kuma kasance masu bunkasa harkokin noma ta cikin Agri-preneurship (L.A.P) da ke da manufar zamarar da matasa da su rungumi sauyin yanayin da ake da shi a bangaren noma ta hanyar basu horo kan yadda za su yi amfani da fasahar zamani wajen morar harkokin noma da samar da ayyukan yi a tsakanin jama’a.”
“A matsayinmu na gwamnati, za mu cigaba da zuba jari a bangaren fasaha da nemi dabaru domin shawo kan matsalolin da ake fama da su a cikin gida.”