ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, June 4, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Tsaka Mai Wuyar Da Masu Gidajen Burodi Ke Ciki A Kaduna – Yarima

by Abubakar Abba
3 years ago
Tsaka

MUHAMMAD ADAM YARIMA, ya shafe akalla sama da shekara 20 yana sana’ar Burodi. A wannan tattaunawa da ya yi da wakilinmu, ABUBAKAR ABBA, ya yi tsokaci a kan kalubalen da gidajen burodi a Jihar Kaduna ke fuskanta, sakamakon tashin gwauron zabi da farashin fulawa ya yi tare da shirye-shiryen da wasu gidajen Burodin ke yi na rufe gidajen da kuma barazanar da ke kunno kai na samun rashin aikin yi da sauran makamantansu. Ga dai yadda tattaunar tasu ta kasance:

Farashin fulawa na ci gaba da hauhawa, wane hali gidajen Burodi suka samu kansu yanzu?

Da farko dai, duk wanda ya kwana ya tashi a Nijeriya, ya san halin da kasar take ciki, domin tun a lokacin da aka ce farashin man fetur ya karu; kusan farashin komai sai da ya karu. Yanzu fulawa ta zama gwal, ba kuma a yin Burodi sai da ita duk da cewa a kwanan baya, an yi kokarin samar da hanyar da za a rika sarrafa Burodin ba tare da dogara da ita ba, amma sai abin ya faskara.

ADVERTISEMENT

 Gaskiyar Magana ita ce, masu gidan Burodi, musamman a nan Jihar Kaduna, suna cikin mawuyacin hali. Fulawar da a baya ake sayen buhunta daya a kan naira 23,000 zuwa 24,000, yanzu ta naira 29,000; wannan mai saukin kudi kenan, amma mai kyau tana kai wa har naira 32,000.

Duba da wadannan matsaloli da ka jero, yanzu wane hali wannan masana’anta take ciki?

LABARAI MASU NASABA

Har Yanzu Ana Yin Allah-wadai Da Cin Amanar Da Aka Yi Wa Kwankwaso – Hon. MB Aliyu

Dalilin Da Ya Sa PDP Ke Cikin Rikici, Za Ta Dawo Da Karfin Ta —Saraki

Ko shakka babu, maganar da ake a halin yanzu gidajen Burodi da dama a jihar na rufe, ba sa iya yin aiki. Sannan, akwai gidajen Burodin da suke a nan cikin kwaryar Kaduna, akalla sun kai kimanin 50 da aka sa su a kasuwa za a sayar. Idan ka ga mutum na aikin Burodi yanzu, babu shakka mai karfin gaske ne, kusan masu karfin a da su ne suka koma kanana yanzu, wani lokacin a yi aiki a samu riba, wani lokacin kuma a samu faduwa, amma

saboda sana’ar da aka iya kenan, shi ya sa ake jurewa ake ci gaba da yi.

Har ila yau, ina tabbatar maka da cewa, ko a yanzu akwai masu gidajen Burodin da suke shirin rufewa. Ba wai maganar fulawa ake yi kadai ba, har da batun duk wani abu da ka sani ana hada Burodin da shi farashinsa ya karu, duk wadannan abubuwa ne wadanda kai tsaye suke shafar masu sana’ar gidajen Burodin.

Idan aka ci gaba da rufe wadannan gidajen Burodi kamar ya ka bayyana, mene ne makomar ma’aikatan da suke yi muku aiki?

Wannan ai a bayyane yake, in dai har za a ci gaba da rufe wadannan masana’antu, ya zama wajibi a samu karancin ayyukan yi, domin idan har kana neman wata hanya da mutane za su taimaki kansu da iyalansu musamman ma matasa, sai ka sama musu abin yi. Wannan sana’a ta Burodi tana matukar taimakawa, musamman a bangaren matasa wajen samun kudaden da za su rika tallafa wa kawunansu, ba tare da dogaro ga wani ko iyayensu ba, wani lokacin ma har ‘yan’uwansu suna taimakawa.

Haka nan kuma, yanayin da ake ciki yanzu ya sa masu gidajen Burodin ba su da wani zabi, illa kara farashin kudin Burodin; domin a halin da ake ciki, sai dai kawai a ce innalillahi wa’inna ilaihir raji’un. Domin kuwa yanzu, idan za ka yi tuwo a gidanka, sai ka kashe kusan akalla naira 2,000, amma idan kana da Burodinka da dan kayan shayi, komai sai ya ishe ku. Yanzu idan mun kara wa Burodin farashi, wane irin yanayi kenan mutane za su shiga.

Shi kansa mai sana’ar Burodin da ya zamar masa dole ya kara farashin Burodin sai abin ya shafe shi, domin idan har mutane suna kara bukatar Burodin, gidajen Burodin kasuwarsu za ta kara yin sama. Amma idan ta kai mutane ba sa iya saye saboda karin farashi kasuwar za ta yi kasa, idan kuma kasuwar ta yi kasa sarrafa Burodin shi ma zai yi kasa, kuma ba lallai ba ne a samu kudin da har za a iya juyawa a yi  wani aikin daban ba.

Ina mafita dangane da wadanan dinbin matsalolin da ka ambata?

Mafitar ita ce, gaskiya dai kusan sai gwamnati ta kawo mana daukin gaggawa a wannan fani, domin idan akwai wata sana’ar da ake yi yanzu a kasar nan, wadda ba a tsayawa ana jiran gwamnati, kusan zan iya cewa ita ce wannan sana’a ta Burodi; domin kuwa tana daya daga cikin sana’oin da zai yi wuya ka ji an ce wani mai gidan Burodi ya je ya roki gwamnati ta taimaka masa da wani abu, sai dai ma su masu gidan Burodin ne suke taimaka wa gwamnatin, wajen sama mata da kudaden shiga da daukar marasa aikin yi, musamman matasa da sauransu.

Babbar masalahar da za a iya cimma kan wadannan matsaloli su ne, ya zama wajibi gwamnatoci, musamman gwamnatin tarayya ta yi hobasa wajen kawo wa gidajen Burodi daukin gaggawa, domin a gaskiya muna bukatar tallafi, idan kuma har aka bar mu a cikin wannan yanayi, tabbas su ma sauran al’umma za su fada cikin irin yanayin da muke ciki.

Sannan, kar a manta al’umma sun zabi wannan gwamnatin ne, bisa yakinsu na za su samu saukin rayuwa na yanayin da suke a ciki. Tabbas ya zama wajibi, gwamnati ta tallafa wa masu gidajen Burodi, domin mu ba masu dogon buri ba ne, duk yadda aka tallafa mana in sha Allah za a ga sauyi. A yanzu masu gidajen Burodi bukatarsu; ba wai lallai samun wata kazamar riba ba ce illa kawai; mu samu kudi mu kara juya su a cikin sana’ar.

Har wa yau, idan kana neman wanda ake bi bashi a halin yanzu, in ka samu mai gidan Burodi magana ta kare, saboda masu sayar mana da fulawa suna yin kokari matuka, domin za su iya ba ka bashin buhun fulawar da za ka iya samu ka yi aiki, idan bashin masu ba mu fulawar ya yi yawa a kanmu, a karshe muka gaza biya, sai dai a sayar da gidan Burodin a biya bashin. Saboda haka, ka ga akwai matsala, shi yasa akwai matukar bukatar gwamnati ta kawo mana dauki ta hanyar tallafa mana, domin mu samu mu fita daga cikin wannan yanayi da muke ciki.

Tsaka
Abubakar Abba
+ postsBio
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Abin Da Ya Sa Gwamnatin Taraba Ta Sayo Sabbin Kayan Noma Na Zamani
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Kamfanin Simintin Ɗangote Ya Ƙaddamar Da Shirye-shiryen Tallafa Wa Mazauna Jihar Biniwe
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Dalilin Gwamnatin Kwara Na Zuba Dala Biliyan 70 A Fannin Kiwon Dabbobi
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Cibiyar IAR Ta Gudanar Da Ayyukan Bincike 140 Kan Sabbin Amfanin Gona 

MASU ALAKA

Har Yanzu Ana Yin Allah-wadai Da Cin Amanar Da Aka Yi Wa Kwankwaso – Hon. MB Aliyu
Tattaunawa

Har Yanzu Ana Yin Allah-wadai Da Cin Amanar Da Aka Yi Wa Kwankwaso – Hon. MB Aliyu

April 10, 2026
 Saraki Zai Jagoranci Kwamitin Gyara Jam’iyyar PDP 
Tattaunawa

Dalilin Da Ya Sa PDP Ke Cikin Rikici, Za Ta Dawo Da Karfin Ta —Saraki

April 4, 2026
Zan Hada Hannu Da Gwamnati Wajen Bunkasa Yanki Na —Sarkin Tilden Fulani
Tattaunawa

Zan Hada Hannu Da Gwamnati Wajen Bunkasa Yanki Na —Sarkin Tilden Fulani

March 28, 2026
Next Post
Bayan Sace Fiye Da Mutum 100 A Zamfara: Kauyukan Da ‘Yan Bindiga Suka Sanya Wa Haraji Na Fuskantar Barazana

Bayan Sace Fiye Da Mutum 100 A Zamfara: Kauyukan Da 'Yan Bindiga Suka Sanya Wa Haraji Na Fuskantar Barazana

LABARAI MASU NASABA

Gwamnatin Tarayya Ta Mayar Da Ofishin NAGGW Zuwa Kano Domin Yaƙi Da Hamada

Gwamnatin Tarayya Ta Mayar Da Ofishin NAGGW Zuwa Kano Domin Yaƙi Da Hamada

June 4, 2026
Mambobin NYSC 4, Soja da Mutum 1 Sun Rasu A Hatsarin Mota A Adamawa

Mambobin NYSC 4, Soja da Mutum 1 Sun Rasu A Hatsarin Mota A Adamawa

June 4, 2026
Sarki Sanusi II Ya Tuɓe Rawanin Mai Unguwar Rikadawa Kan Badaƙalar Fili

Sarki Sanusi II Ya Tuɓe Rawanin Mai Unguwar Rikadawa Kan Badaƙalar Fili

June 4, 2026
Tawagar Masanan Dakile Yaduwar Cututtuka Ta Sin Ta Isa DR Congo

Tawagar Masanan Dakile Yaduwar Cututtuka Ta Sin Ta Isa DR Congo

June 3, 2026
Uba Sani Ya Sanya Hannu Kan Sabbin Dokoki A Bangaren Sauya Fannin Wuta, Noma, Da Muhalli

Uba Sani Ya Sanya Hannu Kan Sabbin Dokoki A Bangaren Sauya Fannin Wuta, Noma, Da Muhalli

June 3, 2026
Han Zheng Zai Halarci Taron SPIEF Karo Na 29 A Rasha Tare Da Gudanar Da Ziyarar Aiki A Belarus

Han Zheng Zai Halarci Taron SPIEF Karo Na 29 A Rasha Tare Da Gudanar Da Ziyarar Aiki A Belarus

June 3, 2026
Majalisa Ta Nemi Tinubu Ya Canza Dabarun Yaƙi Da Ta’addanci Don Kawo Ƙarshen Kashe-kashe

’Yan Majalisar Tarayya 3 Sun Fice Daga APC Zuwa ADC da PRP

June 3, 2026
An Fara Watsa Shirye-Shirye Masu Taken “Sha’awar Xi Jinping Ga Al’adu” Da Sauran Fina-Finan Bayyana Labaran Sin A Kasar Laos

An Fara Watsa Shirye-Shirye Masu Taken “Sha’awar Xi Jinping Ga Al’adu” Da Sauran Fina-Finan Bayyana Labaran Sin A Kasar Laos

June 3, 2026
Tambuwal Ya Jajanta Wa Waɗanda Harin ’Yan Bindiga Ya Shafa A Sokoto, Ya Nemi A Ƙara Tsaro

Tambuwal Ya Jajanta Wa Waɗanda Harin ’Yan Bindiga Ya Shafa A Sokoto, Ya Nemi A Ƙara Tsaro

June 3, 2026
Gwamnatin Beijing Ta Amince Da Kafa Cibiyar Kirkire-Kirkiren Fasahar Lissafi Mai Nasaba Da Sararin Samaniya

Gwamnatin Beijing Ta Amince Da Kafa Cibiyar Kirkire-Kirkiren Fasahar Lissafi Mai Nasaba Da Sararin Samaniya

June 3, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.