Kotun daukaka kara da ke Abuja, ta bayyana ranar Talata 5 ga watan Disaman 2023, a matsayin ranar da za ta yanke hukunci kan daukaka karar da ‘yar takarar kujerar gwamna ta jam’iyyar APC, Aishatu Dahiru Binani a zaben 2023 ta yi.
Binani ta shigar da kara kotun daukaka karar tana mai kalubalantar gwamna Ahmadu Umaru Fintiri, INEC da jam’iyyar PDP, biyo bayan hukuncin kotun sauraren kararrakin zaben kujerar gwamna a jihar da ta yi watsi da kokenta.
- Ranar Nakasassu: Gwamna Uba Sani Ya Nanata Kudirin Shigar Da Su Harkokin Jihar Kaduna
- SERAPÂ Ta Nemi Majalisa Ta Yi Watsi Da Bukatar Gina Wa Shettima Gidan Naira Biliyan 15
Haka kuma koton daukaka karar za ta yanke hukunci kan daukaka karar da Honarabul Umar Abdullahi, na jam’iyyar APC, kan Honarabul Calvin Kefas, na jam’iyyar PDP da hukumar zabe INEC kan kujerar dan majalisar dokokin jiha mai wakiltar karamar hukumar Toungo.