Tsohon gwamnan jihar Neja, Dr. Muazu Babangida Aliyu, ya bayyana yadda ya fatattaki shugabannin kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau da Abu Qaqa, daga jihar Neja a wa’adinsa na farko a matsayin gwamnan jihar, inda ya ce, sun shirya mayar da jihar Hedikwatarsu.
Ya ce, shirin magance kalubalen tsaro da ke addabar Nijeriya, kamar ta’addanci da fashi da makami, shiri ne da yake bukatar tanadi mai zurfi ta hanyar kawar da adadin yara miliyan 20 da ba su zuwa makaranta su koma makaranta domin ceto Nijeriya daga matsayin kasa mafi talauci nan gaba.
- Yadda Matakin Raya Kauyuka Da Sin Ta Dauka Ke Taimakawa Kawar Da Talauci Da Ma Yayata Aladun Kasar
- Shirin Rage Tsadar Rayuwa: Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Biyan Sabon Tsarin Albashi Daga Afrilun 2024 – Minista
Dr. Aliyu ya bayyana haka ne a jihar Kaduna a karshen mako lokacin da ya bayyana a matsayin babban bako mai jawabi na shekara ta 2023, wanda cibiyar hulda da jama’a ta Nijeriya (NIPR), reshen Jihar Kaduna ta shirya.
Tsohon gwamnan ya ce, “Babban manufar gwamnati ita ce tsaron rayuka da dukiyoyin ‘yan kasarta, wanda mafi yawan gwamnonin jihohi ba sa daukarsa da muhimmanci. A matsayinka na Babban Jami’in Tsaro na jiharka, bai dace ka yi da’awar gazawa kan tsaron mutananka ba. Eh, mai yiwuwa ne jami’an hukumomin tsaro da ake turowa ba daga jiharka suka fito ba, jami’an gwamnatin tarayya ne da aka turo domin su taimaka wa jiharka.
“Kasancewarka shugaba mai kishin jama’arka, yana taimakawa sosai. A lokacin da na zama Gwamnan jihar Neja, na samu kalubalen tsaro ta hanyar wasu mutane tara da suka je wani kauye a karamar hukumar Mokwa, wadanda suka ninka a shekarar 2007 zuwa mutum 7,000 kuma suna yin fashi da makami da sace mata a yankin. Nan da nan Suka zama wata babbar runduna.
“Na kuma gano cewa wasu gwamnoni (makwabtan Neja) da dama sun yi kokarin yin wani abu akan lamarin amma wata kila suna shakkar tunkarar Shugaban kasa. Hasali ma, jami’an hukumar shige-da-fice guda biyu da aka turo domin su binciki ayyukan kungiyar, sun rikide sun zama mambobin kungiyar. Lokacin da muka gudanar da bincike, sai muka gano cewa sama da kashi 60 cikin 100 na ‘yan kungiyar ba ‘yan Nijeriya ba ne. Asalin Shekau da Abu Qaga su ne shugabannin kungiyar. Na samu goyon bayan Marigayi Shugaban Kasa, Musa Yar’adua cewa, mu maida kowa garinshi sannan aka kai ‘yan kasashen waje iyakokin kasashensu.
“Kila wannan matakin ne ya ceto jihar Neja daga zama tushen Boko Haram. Kamar yadda muka sani, suna ziyartar gadar kogin Neja akai-akai. Babu shakka Gwamnatin Tarayya za ta goyi bayan duk wani Gwamna da ya ke kokarin sauke nauyin da ke wuyansa na kare rayuka da dukiyoyin al’umma” Inji shi.