A yau 4 ga wata ne shugaba Xi Jinping ya aike da wasikar taya murna ga taron dandalin tattaunawa na kasa da kasa na Congdu na 2023.
Xi Jinping ya yi nuni da cewa, tun bayan da aka kafa dandalin na kasa da kasa na Congdu, taron ya tattaro masu basira daga ko’ina a fadin duniya, domin tattauna batutuwa da dama da suka shafi zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya, da ci gaban tattalin arziki mai dorewa, da musayar al’adu da koyi da juna, kuma ya taka kyakkyawar rawa wajen inganta hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa da inganta ra’ayoyin mutane. Xi Jinping ya yi fatan dukkan bakin da suke halartar taron za su zurfafa tunani, da karfafa yin hadin gwiwa na gaskiya tsakanin bangarori daban-daban, da ba da gudummawa wajen raya al’umma mai makomar bai daya ga bil’adama.
A wannan rana ne aka bude taron dandalin tattaunawa na kasa da kasa na Congdu na shekarar 2023 a birnin Guangzhou na lardin Guangdong da ke kudancin kasar Sin, inda aka mayar da “Ra’ayin bangarori daban-daban: Karin Musanya, karin hulda tsakanin Jama’a, da karin hadin gwiwa” a matsayin babban takensa. (Yahaya)