Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC mai mulki, Asiwaju Bola Tinubu, na kan hanyarsa ta dawo wa Nijeriya daga kasar Faransa.
A baya LEADERSHIP ta rawaito cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC na kasa ya tafi kasar Faransa a ranar 27 ga watan Yuni domin yin wata “muhimmiyar tafiya”, kamar yadda ofishin yada labaransa ya bayyana.
- Tinubu Ya Amince Zai Dauki Musulmi A Matsayin Mataimakinsa —Ganduje
- Tinubu Gogaggen Dan Siyasa Ne, In Ji Ganduje
A yammacin ranar Juma’a, Tinubu a shafukansa na sada zumunta da aka tabbatar an wallafa wani bidiyo mai taken, “Zuwa gida… #CityBoy.”
Yayin da yake kasar Faransa, gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun, ya ziyarci Tinubu a kasar Faransa.
Haka kuma, hamshakin attajirin dan kasuwa, Femi Otedola, ya kai wa Tinubu ziyara, inda ya yi addu’ar Allah ya sa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC ya zama shugaban Nijeriya a 2023.
Akwai kuma rahotannin da ke cewa Tinubu ya gana da gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, a birnin Paris, amma kusan nan take masu kula da kafafen yada labarai na Tinubu suka karyata rahoton.