• English
  • Business News
Tuesday, November 4, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kasafin 2024 Ya Bada Fifiko Ne Wajen Jaddada Ajandar Saisaita Nijeriya – Minista

by Sulaiman
2 years ago
Minista

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ce Kasafin Kuɗi na shekarar 2024 ya nuna lallai an fara taka tsanin samun nasarorin ƙudirorin sake bunƙasa ƙasa a ƙarƙashin Ajandar Saisaita Nijeriya ta Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Ministan ya bayyana haka ne a ranar Asabar a Kaduna, yayin da ya ke jawabi a taron shekara wanda Cibiyar Faɗakar Da Jama’a ta Nijeriya (NIPR), reshen Jihar Kaduna, ta shirya.

  • SERAP  Ta Nemi Majalisa Ta Yi Watsi Da Bukatar Gina Wa Shettima Gidan Naira Biliyan 15
  • Bayan Sace Fiye Da Mutum 100 A Zamfara: Kauyukan Da ‘Yan Bindiga Suka Sanya Wa Haraji Na Fuskantar Barazana

Ya ce baki ɗayan kasafin 2024 an bijiro da shi ne bisa zurfafa nazarin manya da ƙananan ƙalubalen da ke fuskantar ƙasar nan, don haka ne aka tsara kasafin yadda zai fara da zaburar da hanyoyin bunƙasa ƙasa da kawo cigaba mai ɗorewa, inganta tattalin arziki da kuma wanzar da yalwar arziki a ƙasa baki ɗaya.

Ya ce: “A cikin wannan satin ne Shugaba Bola Tinubu ya gabatar da Kasafin Kuɗi na 2024 na naira tiriliyan 27.5 ga Majalisar Tarayya, wanda shi ne kasafinsa na farko tun da ya kama mulkinsa. Kasafin kamar yadda ya gabatar da shi, bigire ne na fara taka tsanin tabbatar da cin nasarar Ajandar Saisaita Nijeriya, ta hanyar bada fifiko ga ƙudirorin gina ingantaccen tattalin arziki.

“Sannan kuma kasafin ya nuna yadda gwamnatin Tinubu ke taka-tsantsan da tsantseni wajen bada fifikon kashe kuɗaɗe a hanyoyin da su ka dace, domin ta hakan ake gina ginshiƙin tsarin tattalin arziki mai nisan zango.

LABARAI MASU NASABA

Kalaman Trump A Kan Nijeriya Abun Damuwa Ne – Peter Obi 

Natasha Ta Zargi Akpabio Da Sanya Jami’an Tsaro Su Ƙwace Mata Fasfo A Filin Jirgin Saman Abuja 

“Yayin da Kasafin Kuɗi na 2024 ya tafi hannun majalisa domin yin nazari da tsettsefe shi, mu na da kyakkyawan yaƙinin cewa kasafin zai kasance matakin farko na bin turbar saisaita Nijeriya, kawo cigaba da inganta rayuwar ‘yan Nijeriya.”

Haka kuma Ministan ya ce kafin Shugaba Tinubu ya gabatar da kasafin, sai da ya yi ƙwarya-ƙwaryan kasafi, ya sa wa ƙudirori hannu sun zama doka, kuma ya kafa kwamitin shugaban ƙasa kan tsare-tsaren kuɗaɗe da tattalin arziki, kwamitin iskar gas (CNG), Shirin Bunƙasa Abinci, Shirin Tallafa wa Matsakaita da Ƙananan Masana’antu (MSME) da sauran fannoni masu muhimmanci wajen raya tattalin arziki.

Ya ce: “Muradin da ake so a cimma shi ne samar wa ɗan Nijeriya rayuwa cikin sauƙi, tare da gina tushen dawwamammen yalwar arziki.”

Ya ce tilas fa sai ‘yan Nijeriya sun bai wa wannan gwamnati uzirin cewa ta kama mulki a wani mawuyacin hali ne, amma kuma duk da haka shi Shugaban Ƙasa ya tarbi gaban kowane ƙalubalen da ake tunkara ko ya ke tunkaro ƙasar nan.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Kalaman Trump A Kan Nijeriya Abun Damuwa Ne – Peter Obi 
Manyan Labarai

Kalaman Trump A Kan Nijeriya Abun Damuwa Ne – Peter Obi 

November 4, 2025
Jami’an Tsaro Sun Dawo Da Fasfo Ɗin Sanata Natasha Bayan Ƙwace Shi A Abuja
Manyan Labarai

Natasha Ta Zargi Akpabio Da Sanya Jami’an Tsaro Su Ƙwace Mata Fasfo A Filin Jirgin Saman Abuja 

November 4, 2025
Masu Kashe Mutane A Kudu Maso Gabas Kiristoci Ne – Soludo
Manyan Labarai

Masu Kashe Mutane A Kudu Maso Gabas Kiristoci Ne – Soludo

November 4, 2025
Next Post
Kotu Ta Umarci Dawo Da Motoci 50 Da Tsohon Gwamnan Zamfara Ya Kwashe

Kotu Ta Umarci Dawo Da Motoci 50 Da Tsohon Gwamnan Zamfara Ya Kwashe

LABARAI MASU NASABA

Dalilin Da Ya Sa Sanatoci Ba Su Goyi Bayana Ba Lokacin Da Aka Dakatar Da Ni – Natasha

Dalilin Da Ya Sa Sanatoci Ba Su Goyi Bayana Ba Lokacin Da Aka Dakatar Da Ni – Natasha

November 4, 2025
Kalaman Trump A Kan Nijeriya Abun Damuwa Ne – Peter Obi 

Kalaman Trump A Kan Nijeriya Abun Damuwa Ne – Peter Obi 

November 4, 2025
Jami’an Tsaro Sun Dawo Da Fasfo Ɗin Sanata Natasha Bayan Ƙwace Shi A Abuja

Natasha Ta Zargi Akpabio Da Sanya Jami’an Tsaro Su Ƙwace Mata Fasfo A Filin Jirgin Saman Abuja 

November 4, 2025
Masu Kashe Mutane A Kudu Maso Gabas Kiristoci Ne – Soludo

Masu Kashe Mutane A Kudu Maso Gabas Kiristoci Ne – Soludo

November 4, 2025
Ribadu Ya Gana Da Hafsoshin Tsaro Biyo Bayan Kalaman Trump 

Ribadu Ya Gana Da Hafsoshin Tsaro Biyo Bayan Kalaman Trump 

November 4, 2025
Sarkin Kasar Spaniya Zai Kawo Ziyara Kasar Sin

Sarkin Kasar Spaniya Zai Kawo Ziyara Kasar Sin

November 3, 2025
Sin Ta Yi Watsi Da Zargin Trump Dangane Da Gwajin Nukiliya A Asirce

Sin Ta Yi Watsi Da Zargin Trump Dangane Da Gwajin Nukiliya A Asirce

November 3, 2025
An Bude Taron Kasuwanci Na Duniya Na 18 A Macau

An Bude Taron Kasuwanci Na Duniya Na 18 A Macau

November 3, 2025
“Ƴan Adawa Sun Wuce Gona da Iri — Wike Ya Soki Masu Goyon Bayan  Trump

“Ƴan Adawa Sun Wuce Gona da Iri — Wike Ya Soki Masu Goyon Bayan  Trump

November 3, 2025
Shugabannin Wasu Kasashe Za Su Halarci Baje Kolin CIIE Karo Na Takwas A Birnin Shanghai

Shugabannin Wasu Kasashe Za Su Halarci Baje Kolin CIIE Karo Na Takwas A Birnin Shanghai

November 3, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.