Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya gabatar da naira biliyan 207,750,200,00.00 a matsayin kasafin kudin shekarar 2024.
Kasafin da aka yi masa take domin daurawa daga na baya, an ware naira biliyan N87,250,200,000.00 kwatankwacin kaso 42 cikin dari a matsayin na gudanar da ayyukan yau da gobe, yayin da kuma aka ware N120,500,000,000.00 domin gudanar da manyan ayyuka, wato kwatankwacin kaso 58 cikin ɗari dari na kasafin kudin.
- Kotu Ta Yi Wa Mutane 4 Daurin Rai Da Rai Bisa Samun Su Da Laifin Daukar Nauyin Boko Haram
- Kasafin 2024 Ya Bada Fifiko Ne Wajen Jaddada Ajandar Saisaita Nijeriya – Minista
Da ya ke miƙa daftarin kasafin ga majalisar dokokin jihar Gombe a ranar Litinin, Gwamna Inuwa, ya shaida cewar kasafin an tsara shi ne domin cigaba da daurawa daga nasarorin da gwamnatin ta samu a zangonta na farko.
A kasafin, an ware wa ɓangaren ilimi, lafiya, bunƙasa harkokin mata da matasa gami da tsaron cikin gida muhimman kaso a cikin kasafin.
A kasafin na 2024 an ware wa bangaren noma da kiwo N7,366,000,000.00, kasuwanci, masana’antu, da yawon buɗe ido N3,510,000,000.00, ayyuka, gidaje da sufuri N50,962,500,000.00, Land Administration: N1,980,000,000.00, albarkatun ruwa, muhalli da albarkatun dazuka: N18,365,600,000.00, kimiyya, fasaha da kere-kere N169,100,000.00.
Sauran ɓangarorin sun hada da ilimi N8,103,800,500.00, ilimi a manyan matakai N5,768,000,000.00, kiwon lafiya – N5,953,200,500.00; matasa da wasanni – N2,460,000,000.00; harkokin mata da walwalar jama’a – N1,197,500,000.00; ƙananan hukumomi da bunƙasa ci gaban al’mma – N130,000,000.00- tsaron cikin gida – N550,000,000.00; yada labarai, al’adu – N805,000,000.00; ayyukan komai da ruwanka – N3,879,500,000.00; doka da shari’a – N2,426,800,000.00.
Gwamnan ya sanar da cewa, gwamnatin jihar ta maida hankali wajen ganin dukkanin abubuwan da aka tsara an samu nasarar cimmawa domin tabbatar da cigaban jihar da al’ummar jihar baki daya.
Gwamnan ya gode wa majalisar dokokin jihar bisa haɗin kai da suke bai wa gwamnatinsa domin cigaban jihar.
A nasa bangaren, kakakin majalisar dokokin jihar Gombe, Rt. Honourable Mohammed Abubakar Luggerewo, ya bada tabbacin cewar mambobin majalisar za su yi aikin duba kasafin domin hanzarin amincewa da shi domin bada damar aiwatar da tsare-tsaren da aka tsara.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp