Taron Saudi Green Initiative (SGI) na gudana karo na 28 da hadin guiwa da Majalisar Dinkin Duniya kan sauyin yanayi (COP28), wanda ya samar da dandalin tattaunawa tsakanin masu ruwa da tsaki da dama don kawo dakile matsalar sauyin yanayi. Â
Mai Martaba Mohammed bin Salman bin Abdulaziz Al Saud, yarima mai jiran gado, kuma shugaban kwamitin koli na inganta koren yanayi a Saudiyya ne ya kaddamar da shirin na Saudiyya Green Initiative a shekarar 2021.
- Nijeriya Ta Sake Bukatar Sojin Nijar Su Saki Bazoum
- Gwamnan Gombe Ya Gabatar Da Naira Biliyan N207.75bn A Matsayin Kasafin 2024
A taron SGI, jami’an Saudiyya sun mayar da hankali kan ci gaban da ake samu kan burin Masarautar na cimma matsaya mai kyau nan da shekarar 2060.
Manufofin taron shi ne samar da yanayi na duniya ta hanyar aiwatar da tsare-tsare sama da 80 na jama’a da na kamfanoni masu zaman kansu da ke wakiltar zuba jarin sama da dalar Amurka biliyan 188, don samar da kyakkyawar makoma ga kowa.
Saudiyya na son cimma burinta na rage hayakin Carbon da tan miliyan 278 a kowace shekara nan da shekarar 2030.
Masarautar na da nufin yin cimma daidaiton makamashi don samar da wutar lantarki ta hanyar samun iskar gas da makamashi da kusan kashi 50 nan da shekarar 2030.
Sama da tsare-tsare 40 sun riga sun fara aiki, wanda ke tallafawa kai tsaye ga ci gaban da ke na dasa itatuwa miliyan 600 da kuma gyara wasu miliyan takwas nan da shekarar 2030.
A yanzu za a aiwatar da dabarun inganta dazuka da kuma gyara ciyayi da furanni don magance matsalar sauyin yanayi da duniya ke fama da shi a yanzu.
Za a aiwatar da taswirar bishiyoyi biliyan 10 a matakai biyu; kashi na farko (2024-2030), zai mayar da hankali kan yanayin muhalli. Mataki na biyu zai habaka yunkurin samo dabaru.
Yunkurin da Saudiyya ke yi a fadin Masarautar zai taimaka wajen samar da ayyukan yi a bangarori da dama, tare da taimakawa wajen yaki da kwararowar hamada da yashi, da rage tasirin guguwar kura da inganta rayuwa ga mazauna kasar.
A halin yanzu, kashi 18.1 na filaye da 6.49% na muhallin ruwa a Saudiyya suna samun kariya.
Tattaunawar SGI, wacce aka fara a ranar 30 ga watan Nuwamba, za ta ci gaba da gudana har zuwa karshen ranar 12 ga Disamba.