Babban hafsan sojin kasa (COAS), Laftanar Janar Taoreed Lagbaja, a ranar Talata, ya ziyarci wurin da sojoji suka kai harin bama-bamai a unguwar Tudun Biri da ke karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna.
Hafsan sojojin, da isarsa wurin, ya gana da Dangaladiman Zazzau da Hakimin Rigasa, Architect Aminu Idris, da sauran shugabanni da sauran al’umma.
Shugaban hafsan sojojin ya kuma ziyarci wadanda abin ya shafa a asibitin koyarwa na Barau Dikko da ke Unguwar Rimi a cikin birnin Kaduna.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp