Rundunar ‘yansandan Jihar Kano ta ce ta kama mutane 15 tare da kwato motoci 20 da aka sace a sassan jihar.
Kakakin rundunar ‘yansandan jihar, SP Abdullahi Kiyawa ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata a Kano.
- Kaduna: Muna Neman Afuwar Kisan Masu Maulidi – Hafsan Sojin Kasa
- Tinubu Ya Dawo Abuja Bayan Halartar Taron Sauyin Yanayi A Dubai
Ya ce wannan nasarar ta samo asali ne daga kudurin rundunar na kawo karshen duk wasu laifuka a jihar.
Kiyawa ya ce, “Mun himmatu sosai wajen yakar satar motoci da duk wani nau’in aika-aika a wuraren da muke sa ido.
“A cikin watan da ya gabata, rundunar ‘yansanda ta ci gaba da jajircewar don tabbatar da kare rayuka da dukiyoyin daukacin mazauna jihar nan.”
Ya mika godiyarsa ga jama’ar jihar kan hadin kai da goyon baya da ake ba su.
Kwamishinan ‘yansandan jihar, Usaini Gumel, ya jaddada aniyar rundunar na yin aiki cikin doka.
Ya kuma shawarci jama’ar jihar da suke kai rahoton duk wani mutum ko wani abu da ake zargi ga ofishin ‘yansanda mafi kusa domin daukar matakin tsaro cikin gaggawa.