Wata kungiyar Majalisar matasan Nijeriya shiyyar Arewa maso Yamma (NYCN) da kuma kungiyar matasan Arewa (AYM) sun gudanar da zanga-zangar neman ministan tsaro, Muhammadu Badaru ya yi murabus daga mukaminsa a ranar Laraba a zauren majalisar tarayya da ke a Abuja.
Masu zanga-zangar sun bayyana cewa, tsaro a kasar ya tabarbare a karkashin kulawar Badaru, don haka, ba zai iya tafiyar da ma’aikatar ba. Sun yi kira ga shugaba Bola Tinubu da ya zaburar da Badaru ko kuma ya amince da murabus dinsa.
Masu zanga-zangar sun kuma bukaci majalisar dokokin kasar da ta duba ayyukan Badaru domin daukar matakin da ya dace.