A jiya Alhamis ne majalisar gudanarwar kasar Sin ta fitar da wani shiri na inganta yanayin iska a kokarin da kasar ke yi na bunkasa tattalin arziki mai inganci.
Shirin ya kunshi jerin matakai don cimma burin samun shudin sararin samaniya nan da shekara ta 2025, ta hanyar habaka sauye-sauyen masana’antu zuwa masu kiyaye muhalli, da gina makamashi mai tsafta, da habaka tsarin sufuri mai karancin iskar carbon.
- Kamata Ya Yi Kasashe Masu Ci Gaba Sun Cika Alkawarin Da Suka Yi Na Samar Da Kudaden Taimakawa Kasashe Masu Tasowa Wajen Tinkarar Sauyin Yanayi
- Ba Za A Cimma Wannan Yarjejeniya Ba Tare Da Taimakon Sin Ba
Manufar ita ce rage yawan gurabattacen barbashi wato PM2.5 a cikin iska a birane a matakin lardi da kashi 10 cikin dari ya zuwa 2025, idan aka kwatanta da matakin 2020 don rage yawan gurbataccen iska a kowace rana zuwa kashi 1 ko kasa da haka, da kuma yawan fitar da iskar nitrogen oxides da tururin iskar gas da kashi 10 cikin dari.
Shirin ya bayyana yankin Beijing-Tianjin-Hebei da kewayensa, da kuma yankin kogin Yangtze Delta da filin Fenwei, a matsayin muhimman wurare.
Kasar Sin za ta haramta sabbin ayyukan samar da karafa, da hanzarta kawar da tsofaffin fasahohin aiki a manyan masana’antu, da bunkasa masana’antu masu kiyaye muhalli. (Muhammed Yahaya)