A halin yanzu bayanai sun nuna cewa, kayayyakin da Nijeriya ke fitarwa zuwa kasashen waje ya karu zuwa kashi 60 wanda ya yi daidai da naira tiriliyan 10.35 a zango na uku na wannan shekarar 2023.
Wannan yana zuwa ne yayin da huldar kasuwancin da Nijeriya ta yi da kasashen waje ya karu zuwa naira tiriliyan 10.35, kamar yadda Hukumar Kididdiga ta kasa (National Bureau of Statistics) ta bayar da rahoto.
- Satar Danyen Man Fetur Ta Jawo Wa Nijeriya Asarar Tiriliya 4.3 Cikin Shekaru 5
- Gwamnatin Tarayya Ta Kaddamar Da Shirin Noman Rani A Jihar Neja
Kayayyakin da aka fitar ya kai na Naira Tiriliyan 10.35, kayayyakin da aka shigo da su kuma ya kai na naira tiriliyan 8.46, kayayyakin da aka fitar ya karu zuwa kashi 60.78 idan aka kwatanta da yadda yake a zango na biyu na 2023 na Naira tiriliyan 6.44.
“Haka kuma kayayyakin da Nijeriya ke shigowa da su ya karu da kashi 47.70 a zango na biyu na shekarar 2023 (N5.73tn).”
Hukumnar ta kuma bayyana cewa, wadannan karin da aka samu ya faru ne saboda karuwar harkokin kasuwanci da Nijeriya ta samu a tsakaninta da kasashen Spain, India, The Netherlands, Indonesia, da Faransa, inda suke fitar da kayayyaki zuwa kasashensu, yayin da kuma Nijeriya ta shigo da mafi yawan kayayyakin ta daga kasashen China, Belgium, India, Malta, da kuma kasar Amurka.