Biyo bayan harin bom da jirgin sojin Nijeriya ya jefa a kan masu gudanar da bikin Maulidi a Kauyen Tudun Biri da ke Karamar Hukumar Igabi ta Jihar Kaduna, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama. Wakilinmu SHEHU YAHAYA ya ziyarci kauyen tare da samun nasarar tattaunawa da dattijo mai shekara 74 da haihuwa, MALAM MUSA ABUBAKAR wanda ya tsallake rijiya da baya, inda ya bayyana irin abubuwan da ya gani yayin harin na bom. Ga dai yadda tattaunawar tasu ta kasance:
Baba ko za ka bayyana mana sunanka da kuma matsayinka a wannan gari?
Sunana Malam Musa Abubakar, sannan ni dattijo ne mai shekara 74 da hauhawa, a wannan kauye na Tudun Biri aka haifi iyayenmu, haka nan mu ma a nan aka haife mu.
Ko wannan gari yana da tarihin ta’addanci ne?
Ko daya ba ma harka da ‘yan ta’adda, har ila yau kuma ba ma koyi da su, domin kuwa ba halinmu ba ne a nan Tudun Biri.
Ko za ka iya fada mana abin da ya faru a wannan gari?
A gabana abin ya faru a daidai wurin nan (yana mai nuna kusa inda yake zaune), kujerata tana kusa da wurin da ake taron Maulidin ina zaune, saboda ni ne mutum na farko da ya fara zuwa wurin wannan taro. Sannan, yaran da aka kashe ina zaune suka zo, can sai na ji wani abu ya yi sama ya yi kara, sai aka zo aka ce min, Baba ba ka ji rauni ba? Sai na ce a’a babu abin da ya same ni, domin babu rauni a jikina; haka na tashi na kakkabe babbar rigata na mike, sai dan wannan jinin da kuke gani a jikin rigar tawa shi kadai ne abin da na san ya faru da ni.
Ka ga wani gida can (yana nuna wani gida da ke gabansa)? To akwai mutum bakwai da suka mutu a gidan, wancan gidan kuma da kuke gani; shi ma akwai mutum guda bakwai da suka mutu a gidan. Haka zalika, akwai wata mata da ta mutu tana rike da dan jariri a jikinta, ni na shiga cikin gidan da kaina na cire shi a jikin uwar tana rike da shi a kirjinta, sai dai ita uwar ta rasu; amma jaririn na nan a raye.
Yanzu mene ne kokenku ko bukatarku ga gwamnati?
Muna bukatar gwamnati ta dube mu da idon rahama ta dauki dukkanin irin matakin da ya dace, domin kuwa mu dai ba za mu tashi daga wannan kauye ba, muna nan zama daram. Sannan kuma, ‘yan ta’adda; sun sha zuwa wannan kauye suna kashe mana mutane tare da sace su, har sai mun biya kudin fansa ka a kai ga sakin su.
A shekarun baya, sun kashe mana mutum hudu; amma wannan bai sa mun tashi daga wannan gari ba, sannan babu dama iyalanmu su tafi gona, domin cire amfani ba tare da sun far musu ba, saboda haka garinmu ba daji ba ne. Akwai lokacin da suka turo tumakinsu cikin garin nan yaranmu suka mayar musu da su, saboda ba namu ba ne. Har ila yau, hatta mabiya addinin Kirista da muka gayyata suka halarci wannan taron Maulidi, su ma sun rasa nasu rayukan.
…An Kashe Mana Yara 12 A Gidanmu Kawai – Mista John
Shi ma a zantawarsa da LEADERSHIP Hausa, jagoran mabiya addinin Kirista a Kauyen Tudun Biri, Mista John ya bayyana cewa; yara 12 ne a gidansu suka rasa rayukansu.
Mista John wanda ya bayyana cewa saboda zaman lumana da suke yi a tsakanin Mabiya addinai a Tudun Biri, idan musulmi suna bukukuwan addini sukan halarta.
Ga bayanansa:
“Yarana guda shida, uku mata uku maza da kuma shida na ‘yan’uwana, maza hudu mata biyu dukkanninsu sun mutu a nan take .”Wannan abu ya faru ne a lokacin da mu mabiya addinin Kirista muka zo wurin da ake yin taron Maulidi. Muna tare da su, sai kawai muka ji wani abu ya yi kara, daga baya muka ga ana kuka ana gudu, a takaice dai, gidajenmu duk an share su”, a cewar tasa.
John, wanda yake bayani yana kuka, ya ce ba za su taba mantawa da irin wannan rana ba, wadda suka dauke a matsayin ranar bakin ciki a rayuwarsu.
…Yadda Muka Samu Mummunan Labarin Abin – Sarkin Ifira
Har ila yau, LEADERSHIP Hausa ta zanta da Sarkin Ifira, Alhaji Balarabe Garba, inda ya bayyana cewa; zuwa lokacin tattaunawa da shi, sun tantance akalla gawawarki guda 80 da aka yi jana’izarsu, sannan sama da guda 30 suna can a asibiti. Ya kara da cewa, suna nan suna ci gaba da tantance sauran wasu mutanen.
“Ina gida da misalin karfe goma na dare, aka kira ni aka ce da ni wani jirgi ya fadi a wannan gari ya jefa bom yayin taron Maulidi, kuma jirgi ne mara matuki, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.
A bincike da kidaya gawarwakin da muka yi, mun kirga akalla mutane 80, ban da wadanda suke a asibiti kwance; sama da mutum 30, wanda har zuwa wannan lokaci muna ci gaba da tantance su”, in ji Sarkin.
Bugu da kari, Sarkin ya bukaci al’ummar da lamarin ya shafa, da su zauna lafiya da ci gaba da yin addu’o’i, domin samun mafita.
…Wasu Hare-haren Jiragen Sojoji A Kan Fararen Hula
Wannan ba shi ne karo na farko da jiragen jami’an tsaron Nijeriya suke kai hari a kan fararen hula ba, a shekarar 2017 a ranar 17 ga watan Janairu, jirgin saman sojoji ya saki bam a sansaanin ‘yan gudun hiira na kauyen Kala Balge Jihar Borno, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar sama da mutum 200 tare da raunana sama da mutum 90.
Haka kuma a ranar 28 ga watan Fabrairu na shekarar 2018 jirgin saman sojojin Nijeriya ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 20 a wani hari da aka kai a Jihar Borno daga na kuma a ranar 11 ga watan Afrilu 2019 harin jirin sojoji ya yi sanadiyyar mutuwar mutum11 a Jihar Zamfara, wata uku bayan wannan sai gashi a ranar 2 ga watan Yuli 2019 an sake kashe mutum 13 a wani hari da jirgin saman yaki na sojoji ya kai a kan fararen hula a Jihar Borno. Haka kuma a Jihar Borno kuma a ranar 25 ga watan Afrilu na shekarar 2021 harin jirgin saman sojoji ya kashe mutum 30 duk dai a jihar Borno.
Bayani ya kuma nuna cewa, a ranar 16 ga watan Satumba na shekarar 2021 jirgin saman yaki na sojojin Nijeriya ya kashe mutum 9 a Jihar Yobe, sai kuma a ranar 26 ga watan na Satumba 2021 suka sake kai hari inda mutum 6 suka rasa rayukansu, haka kuma a ranar 20 ga watan Afrilu 2022 inda harin jirgin sama ya kashe mutum 6 a Jihar Neja. Daga nan kuma sai ranar 6 ga watan Yuli 2022 inda harin jirin saman yaki na sojojin Nijeriya ya kashe mutum 2.
Hare haren jiragen yaki na sojon Nijeriya kan fararen hula ba su tsaya a nan ba domin kuwa a ranar 17 ga watan Disamba na shekarar 2022 mutum 60 sun mutu sakamakon harin da aka kai musu. Haka kuma a farkon wannan shekarar (ranar 25 ga watan Janairu 2023) an kashe mutum 40 sakamakon harin da jirgin yaki ya kai a kan fararen hula a Jihar Nasarawa, haka kuma a a ranar 5 ga watan Maris 2023 inda mutum uku suka mutu a harin da wani jigin yaki ya kai a kan mutane, daga nan kuma sai harin da jirgin saman sojoji ya kai a ranar 18 ga watan Agusta 2023 inda mutum daya ya mutu.
Sai kuma na ranar Lahadi 3 ga watan Disamba 2023 wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 85 da dama kuma suna kwance a asibiti.