• English
  • Business News
Saturday, November 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

An Yabawa Kasar Sin Bisa Inganta Hadin Gwiwa Tsakanin Kasashe Masu Tasowa Kan Sauyin Yanayi Yayin Babban Taron Sauyin Yanayi Na MDD

by CGTN Hausa
2 years ago
Kasar sin

A safiyar jiya Juma’a 8 ga watan nan ne kasar Sin ta gudanar da wani babban dandalin tattaunawa, kan hadin gwiwar dake tsakanin kasashe masu tasowa, ta fuskar tinkarar sauyin yanayi, mai taken “zurfafa hadin gwiwa a tsakanin kasashe masu tasowa kan sauyin yanayi, da hada hannu da juna, don neman ci gaba ta hanyar rage gurbata iska”.

A gun taron, wakilin musamman na kasar Sin kan batun sauyin yanayi Xie Zhenhua ya bayyana cewa, kasashe masu tasowa su ne suka fi fama da matsalar sauyin yanayi, kasancewar suna da rauni a fannin, da rashin samun isasshen tallafi. Ya ce, kasarsa na ci gaba da amfani da hanyar hada kai tsakanin kasashe maso tasowa, da nufin ba da taimakon zahiri ga sauran kasashe masu tasowa, don inganta sauye-sauyen makamashi, da inganta juriyar yanayi, da kuma inganta ci gaba ta hanyar rage gurbata iska.

  • Amfani Da Fahasa Zai Bunkasa Harkokin Zabe –Agu
  • Rawar Da Nijeriya Ta Taka A Taron Dumamar Yanayi Na Duniya

Mahalarta taron sun yi tsokaci sosai kan kokarin da kasar Sin ta yi, da ma nasarorin da ta samu ta fuskar hadin gwiwar kasashe masu tasowa kan sauyin yanayi.

A nasa tsokaci, ministan albarkatun kasa da sauyin yanayi na kasar Malawi Michael Bizwick Usi, ya ce kasarsa na fuskantar kalubale iri-iri, inda sauyin yanayi ya haifar mata da aukuwar guguwa mai karfi a lokuta daban daban cikin shekaru biyu da suka gabata. Ya kara da cewa, “kasar Sin ta taimaka mana matuka, kana ta yi hadin kai da Malawi, wajen ganin an gina ababen more rayuwa, da hanyoyi, da sauran gine-gine a fannonin kiwon lafiya, da ilimi, wadanda suka dace da sauyin yanayi.”

Har ila yau, a yayin taron, kasar Sin ta rattaba hannu kan wata takardar aiki, game da hadin gwiwa tsakanin kasashe maso tasowa kan sauyin yanayi tare da kasar Chadi, da kuma wasu takardun shaida, na tabbatar da ayyuka game da hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa kan sauyin yanayi, tare da manyan jami’ai daga ma’aikatar muhalli ta Botswana da wasu karin kasashen. (Mai fassara: Bilkisu Xin)

LABARAI MASU NASABA

Kasar Sin Ta Sake Jaddada Cikakken Goyon Bayanta Ga Muhimmiyar Rawar Da MDD Ke Takawa A Harkokin Kasa Da Kasa 

Babban Yankin Sin Da Taiwan Sun Yi Tarukan Bita Don Tunawa Da Taron Xi Da Ma Mai Tarihi

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Kasar Sin Ta Sake Jaddada Cikakken Goyon Bayanta Ga Muhimmiyar Rawar Da MDD Ke Takawa A Harkokin Kasa Da Kasa 
Daga Birnin Sin

Kasar Sin Ta Sake Jaddada Cikakken Goyon Bayanta Ga Muhimmiyar Rawar Da MDD Ke Takawa A Harkokin Kasa Da Kasa 

November 8, 2025
Babban Yankin Sin Da Taiwan Sun Yi Tarukan Bita Don Tunawa Da Taron Xi Da Ma Mai Tarihi
Daga Birnin Sin

Babban Yankin Sin Da Taiwan Sun Yi Tarukan Bita Don Tunawa Da Taron Xi Da Ma Mai Tarihi

November 8, 2025
Firaministan Kasar Georgia: CIIE Muhimmin Dandali Ne
Daga Birnin Sin

Firaministan Kasar Georgia: CIIE Muhimmin Dandali Ne

November 8, 2025
Next Post
Tsaro: Yadda Sojoji Ke Rakiyar Matafiya Tsakanin Gusau Zuwa Dansadau

Tsaro: Yadda Sojoji Ke Rakiyar Matafiya Tsakanin Gusau Zuwa Dansadau

LABARAI MASU NASABA

Kasar Sin Ta Sake Jaddada Cikakken Goyon Bayanta Ga Muhimmiyar Rawar Da MDD Ke Takawa A Harkokin Kasa Da Kasa 

Kasar Sin Ta Sake Jaddada Cikakken Goyon Bayanta Ga Muhimmiyar Rawar Da MDD Ke Takawa A Harkokin Kasa Da Kasa 

November 8, 2025
Turkiyya Na Karbar Bakuncin Wasu Kasashen Musulmai Game Da Makomar Gaza

Turkiyya Na Karbar Bakuncin Wasu Kasashen Musulmai Game Da Makomar Gaza

November 8, 2025
Babban Yankin Sin Da Taiwan Sun Yi Tarukan Bita Don Tunawa Da Taron Xi Da Ma Mai Tarihi

Babban Yankin Sin Da Taiwan Sun Yi Tarukan Bita Don Tunawa Da Taron Xi Da Ma Mai Tarihi

November 8, 2025
Kasashen Afirka Bakwai Da Sojojin Amurka Suka Shiga

Kasashen Afirka Bakwai Da Sojojin Amurka Suka Shiga

November 8, 2025
Firaministan Kasar Georgia: CIIE Muhimmin Dandali Ne

Firaministan Kasar Georgia: CIIE Muhimmin Dandali Ne

November 8, 2025
Yadda Aka Tsara Gudanar Da Gasar Kofin Afirka A Moroko

Yadda Aka Tsara Gudanar Da Gasar Kofin Afirka A Moroko

November 8, 2025
CMG Ya Watsa Jerin Shirye-Shirye Don Tunawa Da Cika Shekaru 80 Da Dawowar Yankin Taiwan Kasar Sin

CMG Ya Watsa Jerin Shirye-Shirye Don Tunawa Da Cika Shekaru 80 Da Dawowar Yankin Taiwan Kasar Sin

November 8, 2025
CMG Ya Gabatar Da Jerin Rahotannin Talabijin Kan Tunawa Da Cika Shekaru 80 Da Dawowar Yankin Taiwan Kasar Sin

CMG Ya Gabatar Da Jerin Rahotannin Talabijin Kan Tunawa Da Cika Shekaru 80 Da Dawowar Yankin Taiwan Kasar Sin

November 8, 2025
Xi Ya Yi Kiran Zurfafa Gyare-gyare Da Bude Kofa A Yayin Rangadin Aiki A Guangdong

Xi Ya Yi Kiran Zurfafa Gyare-gyare Da Bude Kofa A Yayin Rangadin Aiki A Guangdong

November 8, 2025
Ta’aziyyar Rasuwar Jarumin Kannywood, Malam Nata’ala

Ta’aziyyar Rasuwar Jarumin Kannywood, Malam Nata’ala

November 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.