Hukumar dake kula da gasar firimiya ta Ingila tana tuhumar kungiyar Manchester City da laifin kasa tsawatarwa ‘yan wasanta a wasan da suka tashi 3-3 da Tottenham a gasar Premier League.
‘Yan wasan Manchester City sun gewaye alkalin wasa, Simon Hooper, wanda ya bayar da bugun tazara dab da za a tashi a lokacin da kwallo ta je wajen Jack Grealish bayan da ya nufi raga.
- Manchester City Ta Koma Ta Uku A Teburin Firimiya Bayan Buga Canjaras Da Tottenham
- Chelsea Ta Lallasa Tottenham Har Gida Da Ci 4-1
Tun farko Hooper bai busa ketar da aka yi wa Erling Haaland ba, amma kwallo na zuwa wajen dan wasan tawagar Ingila sai kawai ya busa usur domin a dawo a buga ketar da aka yi tun farko.
Haaland yana daga cikin ‘yan wasan Manchester City da suka fi korafi a fafatawar, har ma ya caccaki alkalin wasan a dandalin sada zumunta na D, wanda hakan watakila shi ma ya sa a tuhume shi.
Wasa na uku kenan da tawagar ta Guardiola ta yi canjaras a Premier League a jere, bayan 4-4 da Chelsea, da kuma 1-1 da Liberpool kuma hakan ne ya sa Manchester City ta koma ta ukun teburin babbar gasar kwallo ta Ingila da maki 30, da kuma tazarar maki daya tsakaninta da Liberpool.