Assalamu alaikum masu karatu, barkammu da sake haduwa da ku a wannan makon a cikin shirin namu mai farin jini da albarka na Girki Adon Mace. A yau shafin namu zai yi magana ne akan yadda ake shirya Miyar Hanta.
Ga kuma yadda ake hadawa
Hanta rabin kilo, Attarugu 4, Tattasai 3, Albasa 2, Maggi 5, Gishiri, Citta 3, Tafarnuwa 2, Kori (Curry), Onga fa kuma Man girki.
To ga yadda ake hadawa
Da farko dai uwargida za ki wanke hantar ki yanka daidai misali sai ki sa a tukunyarki ki yanka albasa, kuma ki sanya maggi kwaya daya da dan gishiri, Idan ya yi sai ki sauke ki kwashe a wani kwano, sai ki zuba mai da kayan miyanki ki soya ya soyu da kyau
Idan ya soyu sai ki zuba ruwa kadan ki sa hantar ki kawo Magi, da gishiri, Citta, Tafarnuwa, da kori ki sanya.
Sai ki barshi kamar minti 15, za ki ji gida ya dau kamshi, sai ki sauke. Ita dai wannan miyar za ki iya ci da shinkafa ko Sakwara. A ci dadi lafiya.