Shafin da ke zakulo muku batutuwa daban-daban wadanda suka shafi al’umma, cikin sun hadar da; Zamantakewar Aure, Rayuwar Yau da Kullum, Rayuwar Matasa, Soyayya da dai sauransu.
Tsokacinmu na yau zai yi duba ne game da irin matsalolin da ke afkuwa ga yara mata musamman matasa. Mafi yawan wasu iyayen na sakaci wajen jajircewa a kan ‘ya’yansu ta fannin koya musu yadda za su iya tsaftace jikinsu da kuma tufafinsu hadi da muhallin da suke zaune, tare da sanin lokacin daya kamata a fara koyawa ‘ya’ya mata yadda za su iya girki da sauran abubuwan daya shafi rayuwarsu.
Wanda kuma rashin kulawar ke yawan janyo matsaloli cikin zamantajewar aure har ta kai ga wasu ma su rabu da juna koda kuwa kafin auren sun shafe tsahon shekaru suna zuba soyayya.
Dalilin hakan ya sa shafin Taskira jin ta bakin wasu daga cikin mabiyansa game da wannan batu; Shin laifin waye tsakanin iyayen da ‘ya’yan?, Ko me yake jawo hakan?, Ta wacce hanya ya kamata iyaye su bi wajen ganin sun koyar da ‘ya’yansu mata yadda za su kula da kansu?, Idan namiji ya ci karo da me irin wannan dabi’ar wanne irin mataki ya kamata ya bi, domin magance matsakar?
Ga dai ra’ayoyin nasu kamar haka:
Sunana Aisha Isah Abubakar (Aisha Gama Mai Waka) Jihar Kano:
Magana ta gaskiya laifin iyaye ne, sannan su ma yaran da nasu laifin za ki ga akasarin wasu iyayen ba sa jan ‘ya’yansu a jiki suna nuna musu yadda za su yi a wajan girki, sannan ba sa jan hankalinsu wajan yadda za su kula da mijinsu sannan wasu yaran za ki ga kana kokarin nuna musu abu amma ba sa maida hankali akansa shiririta tayi yawa musamman idan da waya a hannun yarinya, to indai hankalinta yana kai ba za ta yi yadda ake so ba. Idan namiji ya gamu da irin wannan matar to na farko yayi hakuri, sannan idan da hali ya kaita makarantar koyan girki idan me maida hankali ce kuma tana son zaman aurenta za ta maida hankali ta koya, idan kuma taki maida hankali to a samar mata ‘yar uwa ma’ana abokiyar zama sai ta koya mata, ka ga kai ma ka huta da kashe kudin tara. Shawara anan ya kamata iyaye mu maida hankali akan ‘ya’yanmu mu tuna kiwo Allah ya bamu kuma zai tanbaye mu ranar yauma zillu illazillahu mu rike amanar da Allah ya bamu. Su kuma ‘ya’yan su ma su ji tsoran Allah, su tausaya mana su taya mu sauke nauyin da Allah ya dora mana, su rinka jin maganar iyayensu Allah ya shirya mana zuriya baki daya, Allahu a’alam.
Sunana Aminu Adamu Malam Maduri A Jihar Jigawa:
To maganar gaskiya a wannan batu kowa yana da laifi to amma iyaye su ke da babban laifi, domin su ya kamata su na dora su akan hanyar da ta dace, kama daga koya musu girki, tsaftacce muhalli, iya tarbar baki dama kula da Maigida, don haka su ya kamata su na lura da dukkanin abun da ya dace ga yaran su, domin su samu nutsuwa a gidan aure. To ya kamata su ke kiran ‘yan matan duk lokacin da za a gudanar da wani abu mai muhimmanci domin su gani su kuma koya, kuma ya kamata ake ware lokaci wajen koyar da su yadda ake mu’amula a gidan miji da kuma kalubalen dake cikin zamantakewa domin su yi shirin tunkarar sa da kuma magancewa. To magana ta gaskiya duk lokacin da aka ce namiji ya auri irin wannan mata to yayi hakuri da bata gudunmawar da ta dace domin ta koyi wadanan abubuwa, domin ba zai iyu ba ace a lokaci daya za a gyara wannan matsala, don haka dole ayi hakuri da kuma juriya har ta koyi abun da ya dace. To shawara ita ce; da iyaye da ‘yan mata ya kamata su san wannan batu yana da muhimmanci a fannin zaman aure, kuma yana kawo matsaloli da dama a cikin zamantakewar, don haka ya kamata su bashi muhimmanci wajen koyawa ‘ya’yansu abun da ya dace, domin samun nutsuwa a gidan aure.
Sunana Sadiya Garba Kofar Na’isa Jihar Kano:
A gaskiya mafi akasari laifin ya fi ga iyaye, saboda za ki ga iyaye na aikin gida ko girki amma yaransu suna zaune suna danna waya ko suna kallo ba tare da tasa sun zo sun karbe ta ba bare su ma su iya. Abin da ke jawo afkuwar hakan rashin nuna musu tun suna tasowa ta hanyar sasu su share wajen da ki ka bata wajen aikin girki ko kuma zuba wani abu a cikin girki. Hanya mafi sauki ita ce; na farko idan za ki aikin girkin ke ma ki zamo kina tsaftace, sannan wajen girkin shi ma ya zamo a tsaftace, sannan ki sata ta zo ta taimaka miki wajen gyaran kayan girkin, ki nuna mata komai za ta yi ta zamo mai tsaftace komai. Matakin da miji zai dauka shi ne; yayi kokarin nuna mata muhimmancin tsafta a musulunci, sannan bangaren girki ya siyo mata littattafan girke-girke su ma za su taimaka mata, kuma ya dinga nuna mata inba za ta canza ba zai kara aure shi ne; za ta fi dagewa saboda kin san mata bama son kishiya. Shawarar da zan bayar ita ce iyaye mu ji tsoron Allah mu daure mu nunawa ‘ya’yanmu abin da zai kara musu mutunci a gidan mazajensu, domin idan har bakida tsafta baki iya girki ba wallahi Allah sunanki kin rako mata kuma ba kida wata kima gun namiji.
Sunana Alhassan Abdulrahman Bununu Jihar Bauchi:
Wato a gaskiya kowanne bangare suna da laifi, dalili kuwa iyaye su suke da hakki wajan ganin ‘ya’yansu sun kula da tsafta, kula da miji da girke-girke. Wannan ya kamata su nuna musu ne tun suna kanana kafin girma. Su kuma yaran ya kamata su tina ba wai a gaban iyayensu za su dawwama ba gidan wani za su. Hanyar da za a bi shine; su dunga nuna musu tsafta tun suna kanana, su kasance su ma suna kula da iyayensu maza wajan ma’amala, kuma su rinka sasu girki a lokacin da suka samu sararawar makaranta. Matakin da namiji zai bi shi ne; ya nuna fa auren soyayya suka yi da wannan, ya kamata ya dau gyara har ya samo mai koya mata tunda yanzu munada ci gaban wajan koyon girke-girke wannan shi ne hanya mafi sauki. Shawarata ga iyaye da ‘yan mata shi ne; ku maida hankali wajan girki koda kuwa iyayenki suna miki rainon gata ki tuna fa ba a gabansu rayuwarki zai takaita ba, gaba za ki yi, ma’ana gidan wani za ki iyaye kuma su kara kula sosai.
Sunana Hadiza Muhammad Gusau:
Gaskiya a hasashena laifin iyaye ne, dan su yara suna tashi ne akan turbar da iyayensu suka dorasu. Dalilai kuwa su ne; Rashin sanin ya kamata ta bangaren iyaye, da rashin jajircewarsu wurin tarbiyyar yara da kuma horas da su. Hanya mafi sauki shi ne; ‘yarki ta tashi ta ga kina kula da babanta da kuma gidanki ta fannonin tsabtar jiki, tufafi da muhalli. Ta ga kina yawan yin girke-girke kala daban-daban a koda yaushe. Ki kuma ringa sata tana taimaka miki, tun tana karama, kar ki ce sai ta girma, hakan zai sa koda za ta girma abun ya bi jikinta. Ba wai sai an sa ma yarinya ranar aure a ringa kaita wai a koya mata ba, wannan ko kadan ba zai kai ga haihuwar da mai ido ba. Matakin daya kamata ya dauka shi ne; na farko hakuri, sai kuma ya jajirce wurin ganin ta koya. Ta hanyar kaita wuraren koyon wadannan abubuwan ko kuma nemo wacce za ta koya mata, ba tare daya tsangwameta ba. Shawara anan ita ce; kada ace sai aski ya zo gaban goshi za a koya wa yara mata tarbiyyar gidan aure, a’ah! tun farko ya kamata ace an yi haka, ta hanyar horaswa a baki da kuma aikace. Allah ya sa mu dace.
Sunana Ibrahim Isma’il Ibrahim:
To a gaskiya laifin iyaye ne komai a gida ake koyawa idan ba a koya maka a gida ba, ba ta yadda za su iya kamar yadda hausawa suke cewa uban wani baya bawa dan wani lakani sai dai a gida a baka, ta yadda za a bi wurin magance wa shi ne duk lokacin da uwa za ta yi wani abu da zai amfanar da ‘ya’ya to ya kamata a dinga jawo ‘ya’yan a jika su dinga gani ta yadda za su koya. To gaskiya mata duk irin kaunar da namji yake wa mace idan ya zamana ya hada irin abubuwan nan to gaskiya a hankali namiji zai ji kin fita akansa, idan Allah ya hada ni da irin wannan macen to kawai dai zan yi abu daya shi ne hakuri, kuma nayi kokarin ta koyo duk da ba a bari a kwashe duka, kuma su ma ‘ya’ya su maida hankali wurin koya, duk abin da ya dace baka sanin mahimmacin abu sai bakada shi, kuma bukatarshi ta ta sar maka.
Sunana Aisha Abdullahi Jabir Babura:
Laifin ya kasance na duka bangaren ne iyaye da kuma ‘ya’ya. Rashin kula na iyaye ba sa koyawa yarinya tun kafin su aurarta. Kamata yayi tun yarinya tana karama kamar lokacin da ta shiga ‘Junior Secondary’ uwa tana shiga kicin tare da ita tana nuna mata yadda ake girki kala-kala, hakan ne zai sa yarinya ta tashi ta iya girki sosai. Tsafta kuwa shi ma yarinya tana tashi da hakan ne a cikin gidansu, tun yarinya tana karama, ke uwa mace kar ki yarda ta tashi ta ganki da kazanta ko ta tufafi ko ta muhalli, ya kamata iyaye mata su nuna wa yaransu kazanta ba abu bane mai kyau, su nunawa yaransu tsafta ita ce gaba da komai, sannan kuma su ‘kyamaci kazanta su nuna basu sonta koda wasa. Sannan kuma iyaye ya kamata su nuna yaransu aure yana da muhimmanci matuka, iyaye mata ya kamata su yi wa mazanje biyayya sosai yadda yaransu mata za su yi koyi da su, su basu daraja, ku rinka nunawa yaransu shi namiji a sama yake da mace yana da daraja sosai kar su yarda su raina sa. Namiji idan yayi karo da mai irin wannan matsalar, to gaski ya kamata ya dau mataki akan hakan sosai, kar ya sa ido ya kau da shi, saboda wannan babbar matsala ce, musamman idan aka fara haihuwa yara suka fara girma. Ya kamata namiji ya dau kwakkwaran mataki akan hakan. Ya kamata iyaye kafinsu aurar da yarinya su yi kokarin ganin yarinyar su ba ta da wannan matsalar, su tabbatar sun bata tarbiyyar da ya kamata da kuma cewa yarinyar tana da tsafta yadda ya kamata. ‘Yan mata su ma ya kamata su yi kokari su kiyaye wannan matsalolin kafin ayi aure ko bayan an yi aure, bai kamata ba kina mace a ce an sameki irin wannan matsololin gaskiya ‘yan mata kar ku yadda a ce kun rako mata.
Sunana Lawan Isma’il (Lisary) Jihar Kano, Karamar Hukumar Rano:
Mafi akasari matsalar tana faruwa ne daga nuna soyayya ga yaran, ba a son suna shan wahala, su kuma yaran mafiya yawancinsu karance- karancen littafi da kallon fim irin na wannan zamanin ya kan sa su raja’a akan abin da suke gani da kalla. Hanyoyin magance su suna da yawa, amma kadan daga ciki; Uwa tana ware wasu ranaku na bata damar girki kuma kafin nan ma yarinya tun tana karama ya kamata tana sakata dafa abinci, sannan tana nuna mata muhimmancin tsafta ta gida, jiki, da sauransu, sabida addini ma ya zo da maganar tsafta, batun girki kuwa nan ma iyaye suna nunawa yaransu yana daya daga cikin abubuwan da suke saka mata mallakar miji. Da farko a matsayinka na miji ka ci karo da irin wannan tun farkon aurenku ya kamata kana tsayawa kana koya mata ko na ce kuna yi tare sannan cikin fira da zaman takewarku za kana nusar da ita amfanin wadancan abubuwan a zamanta na duniya dama lahira. Shawarata anan ita ce; Babu wasu iyaye ko mazaje ko ma su kansu matan da za su so ace an yi aure an rabu to anan ya kamata yarinya tun tana karama iyaye suna ware wasu lokuta da ma ranaku domin koya musu da kuma basu aikace-aikacen yau da kullum kafin su girma su kai munzalin aure in sha Allah komai zai zo da sauki.
Sunana Sadik Abubakar ‘Yammata, Rijiyar Kano:
Babu shakka wannan matsala babba ce, takan kawo tangarda ga miji da mata. Abin kaico ne a ce mace bata iya wadannan muhimman abubuwa ba, kasancewar su ne sinadaran da ke kawo jin dadi da kwanciyar hankalin ma’aurata. Duk yayin da aka ce mace ta rasa wadannan dabaru, to gaskiya zai yi matukar wahala ta gaza fuskantar wata matsala daga wajen mijinta. Domin kuwa bai samu abubuwan da yake muradi ba, kowane namiji burinsa idan ya kalli matarsa ya ji farin cikin na musamman a ransa. Hakan kuwa ba zai tabbata ba har sai ta mallaki wasu halaye da dabi’u da kuma dabaru, wanda suka hada da tsaftar jikinta da muhalli da gyaran jiki irin na zamani da iya tarairayar miji sannan uwa uba kuma kwarewa a fagen sarrafa tukunya wato girki. Iyaye na ba da gudunmawa sosai wajen faruwar wannan matsala, domin dukkan wadannan abubuwa da aka ambata, yarinya na koyon kaso mafi rinjaye ne a gidansu. Indai har iyaye jajirtattu ne, to hakika ‘yarsu za ta koyi dabarun rike gida tun kafin a kai ta nata gidan. Tun yara suna kanana ya kamata a nuna musu tsafta ita ce mutum, wajibi ne yin tsafta. Idan suka fara tasawa sai a rika nuna musu bambancinsu da maza, idan namiji zai yi wanka sau daya a yini, to ita mace biyu ake bukata ta yi, safe da yamma. Idan Allah ya jarrabi namiji da mace mai wannan siffar, na farko hakuri zai yi. Sai ya dauki matakin sauya ta a hankali, abin da zai iya koya mata da kansa ya koya mata. Wanda kuma ba zai iya ba sai ya nema mata wata cibiya da ake koyar da abin, shikenan sannu a hankali za ta sauya zuwa yadda yake bukata. Iyaye lallai su tabbata yaransu mata sun koyi dabarun zaman gidan aure tun suna gabansu. Wannan ita ce shawara sahihiya, bin ta zai rage yawaitar fuskantar kalubalen da aka ayyana a sama. Allah ya sa mu dace.