A ranar Litinin, yayin wata ziyara da shugaba Bola Tinubu ya kai a birnin Maiduguri na jihar Borno, ya yi ta’aziyya da jajantawa ‘yan Nijeriya da iyalan wadanda suka rasa rayukansu a wani harin bam da rundunar soji ta kai a Tudun Biri da ke jihar Kaduna, inda ya ce akasarin wadanda harin ya rutsa da su sun rasa rayukansu yayin da suke gudanar da taron Mauludi.
Da yake jawabi a fadar Shehun Borno, Alhaji Abubakar Ibn Umar Garbai Al-Amin El-El-Kanemi, Shugaba Tinubu ya yi alkawarin cewa, gwamnatin tarayya za ta ci gaba da yin duk mai yiwuwa wajen bayar da tallafi da kulawa ga iyalan dukkan ‘yan Nijeriya da matsalar rashin tsaro ta shafa a sassan jihar Borno da Nijeriya baki daya.
- Yawan Yaran Da Ke Fama Da Cututtuka Masu Alaka Da Sassan Jiki Masu Taimakawa Numfashi Ya Ragu A Kasar Sin
- Na Samu Farin Ciki Sosai A Farkon Fara Rubutuna – Fauziyya
Tinubu ya bayyana cewa, a karkashin jagorancinsa, al’amuran tsaro za su kasance a kan gaba, ba sai a fagen yaki kadai ba.
A nasa bangaren, Shehun Borno, Alhaji Abubakar Ibn Umar Garbai Al-Amin El-Kanemi ya bukaci shugaban kasar da ya kai ayyukan samar da ababen more rayuwa ga yankunan da ke fama da tashe-tashen hankula na tsawon shekaru.