Sabbin alkaluma da kungiyar masu kera motoci ta kasar Sin ta fitar Litinin din nan na nuna cewa, cinikin motoci a kasar Sin, ya karu da kashi 27.4 bisa 100 kan na shekarar bara, karuwar kashi 4.1 bisa 100 kan na watan Oktoban da ya gabata, inda ya kai motoci miliyan 2.97.
Alkaluman sun nuna cewa, adadin motocin da kasar ta fitar a watan Nuwamba, ya kai miliyan 3.09, wanda ya karu da kashi 29.4 bisa 100 bisa na makamancin lokaci na shekarar bara, da kashi 7 cikin 100, idan aka kwatanta da na watan Oktoba.
A cikin wani rahoto da kungiyar ta fitar, ta bayyana cewa, yanayin kasuwar motoci a watan Nuwamba, ya zarce yadda ake tsammani, inda yawan motocin da aka fitar ya kai wani babban matsayi, yayin da aka sayar da motoci kusan miliyan uku.(Ibrahim)