Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC), ta gurfanar da Aisha Malkohi da ka fi sani da Ummitah, Arab Money da mijinta, Abubakar Mahmoud, bisa laifin damfarar Naira miliyan 410.5.
Hukumar ta gurfanar da Malkohi a gaban wata babbar kotun Jihar Kano, yayin da mijinta ya tsere, a cewar wata sanarwa da EFCC ta fitar a ranar Litinin.
- Cinikin Motoci A Sin Ya Karu Da 27.4% A Watan Nuwamba
- Kowacce Yarinya Za Ta Samu Ilimi Da Sana’a A Jihar Katsina – Gwamnati
Kakakin EFCC, Dele Oyewale, ya bayyana a cikin sanarwar cewa wadda ake tuhuma an gurfanar da ita a gaban kotu bisa tuhume-tuhume biyar da suka shafi damfara na kudade har N410,518,000.
Sai dai kuma ta ce ba ta aikata laifin ba a lokacin da aka karanta mata tuhume-tuhumen a gaban alkalin kotun, Aisha Mahmud.
Hukumar EFCC ta damke wadda ake zargin a Kano, biyo bayan karar da wasu masu shigar da kara guda biyu Farida Ibrahim da Ibrahim Mohammed Abdulrahman suka shigar, inda suke zargin ta hada baki da mijinta suka damfare su.
Masu karar sun ce ta damfare su ta hanyar amshe musu kudi da sunan za ta siyo musu motoci 64, gwala-gwalai, da kayan wuta daga Saudiyya.
Bayan haka ne sai hukumar ta tsunduma farautar su da kuma bin diddigin abin da ya faru.
EFCC ta gano cewa an jibge Naira miliyan 410 a asusun wani kamfani mai suna Golden Grass, wanda mallakin wannan mata ce da mijinta.
Sannan an gano sun rika canja wa kudaden asusun ajiya ta hanyar rarraba su ita da mijinta zuwa wasu asusun ajiyar banki.