• English
  • Business News
Monday, October 27, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kwamitin Majalisar Dattawa Ya Nemi A Karawa Ma’aikatar Yaɗa Labarai Kudi Kan Kasafin 2024

by Sulaiman
2 years ago
Dattawa

Kwamitin Majalisar Dattawa Mai Lura da Harkokin Yaɗa Labarai, ya nuna rashin amincewa dangane da ƙarancin kuɗaɗen da kwamitin ya ce Gwamnatin Tarayya ta ware wa Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da kai, a Kasafin 2024.

Shugaban kwamitin, Sanata Kenneth Eze ne ya nuna damuwa da rashin amincewa dangane da ƙarancin kuɗaɗen, a lokacin da Ministan Yaɗa Labarai, Alhaji Mohammed Idris ya bayyana a gaban kwamitin, domin ya kare kasafin ma’aikatarsa, a ranar Talata, a Abuja.

  • Jamhuriyar Nijar Za Ta Fara Fitar Da Danyen Mai A Watan Janairu
  • Na Samu Farin Ciki Sosai A Farkon Fara Rubutuna – Fauziyya

“Haba jama’a, ai waɗannan kuɗaɗe cikin cokali bai yiwuwa a ce da su kaɗai za a yi amfani har a samu biyan buƙatar yada manufofin ƙasarmu. Muddin waɗannan kuɗaɗen ne aka ware wa wannan ma’aikatar, to ba inda za mu iya cimma gaci. Ta yaya za a iya wayar da kan jama’a ta hanyar yaɗa labarai da kyawawan manufofi da waɗannan kuɗaɗe ƙalilan?

“Ma’aikatar Yaɗa Labarai fa wuri ne mai muhimmancin da wajibi ne a yi wa wurin riƙon kazar kuku, ba riƙon sakainar kashi ba. Ina magana idan har fa ana so a samu biyan buƙatar samun nasarar Ajandar Saidaita Nijeriya da mu ke magana, to dole ma’aikatar yaɗa labarai ce a sahun gaba.

“Wannan ma’aikata ce za ta kasance mai haska wa ƙasar nan fitilar kyakkyawar ɗabi’un jama’ar ta, kuma akwai wawakeken giɓi tsakanin gwamnati da jama’a, wanda wannan ma’aikatar ce tilas za ta iya cike giɓin,” inji sanatan.

LABARAI MASU NASABA

Matatar Dangote Za Ta Faɗaɗa Ƙarfin Aiki Zuwa Ganga Miliyan 1.4 Kullum

“Ba Gudu Ba Ja Da Baya Game Da Tsarin “Call-up system” A NPA”

“Na duba a cikin kasafin, amma ban ga ko sisi da za a kashe a Hukumar Kula da Jaridu ba, ban ga Hukumar APCON ba, kuma ban ga kasafin wasu hukumomin da ke ƙarƙashin wannan ma’aikata ba.

“Shin gwamnati na so ta shaida mana cewa an rushe waɗannan hukumomin kenan, yadda har za su iya aiki ko ba ma’aikata a cikin su?

“Wa zai biya albashin su? Watannin baya ba da daɗewa ba fa aka naɗa wa hukumomin sabbin Manyan Daraktoci da Manyan Sakatarori.

Kenneth ya ci gaba da cewa, “Mai Girma Minista, wannan batu ne fa mai muhimmanci ga wannan kwamiti, kuma tabbas za mu duba wannan lamari.”

A nasa bayanin, Minista Idris ya shaida wa sanatocin cewa za a ƙaddamar da Shirin Cusa Ɗa’a, Kishin Ƙasa da Kyawawan Ɗabi’u (NVC) cikin 2024.

Ya ce akwai gagarimin aiki a gaban ma’aikatar sa wajen tabbatar da samun nasarar shirin cusa ɗa’a da kishin ƙasa, wanda Naira biliyan 1 da aka ware wa ma’aikatar sa, a matsayin kuɗaɗen gudanar da manyan ayyuka, ko kusa ba za su wadata ba.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Matatar Dangote Za Ta Faɗaɗa Ƙarfin Aiki Zuwa Ganga Miliyan 1.4 Kullum
Manyan Labarai

Matatar Dangote Za Ta Faɗaɗa Ƙarfin Aiki Zuwa Ganga Miliyan 1.4 Kullum

October 26, 2025
“Ba Gudu Ba Ja Da Baya Game Da Tsarin “Call-up system” A NPA”
Labarai

“Ba Gudu Ba Ja Da Baya Game Da Tsarin “Call-up system” A NPA”

October 26, 2025
Dalilin Da Suka Sa Hisbah Ta Dakatar Da Auren Ƴan TikTok A Kano
Manyan Labarai

Dalilin Da Suka Sa Hisbah Ta Dakatar Da Auren Ƴan TikTok A Kano

October 26, 2025
Next Post
Shugaba Xi Ya Gana Da Manyan Shugabannin Kasar Vietnam

Shugaba Xi Ya Gana Da Manyan Shugabannin Kasar Vietnam

LABARAI MASU NASABA

Tunawa Da Dawowar Taiwan Kasar Sin Shekaru 80 Da Suka Wuce Yana Da Ma’ana Sosai

Tunawa Da Dawowar Taiwan Kasar Sin Shekaru 80 Da Suka Wuce Yana Da Ma’ana Sosai

October 26, 2025
Matatar Dangote Za Ta Faɗaɗa Ƙarfin Aiki Zuwa Ganga Miliyan 1.4 Kullum

Matatar Dangote Za Ta Faɗaɗa Ƙarfin Aiki Zuwa Ganga Miliyan 1.4 Kullum

October 26, 2025
Kara Bude Kofofin Sin Zai Samar Da Karin Gajiya A Fannin Bunkasar Duniya

Kara Bude Kofofin Sin Zai Samar Da Karin Gajiya A Fannin Bunkasar Duniya

October 26, 2025
“Ba Gudu Ba Ja Da Baya Game Da Tsarin “Call-up system” A NPA”

“Ba Gudu Ba Ja Da Baya Game Da Tsarin “Call-up system” A NPA”

October 26, 2025
Ya Zuwa Satumban Bana Adadin Lantarki Da Sin Ta Samar Ya Karu Da Kaso 17.5%

Ya Zuwa Satumban Bana Adadin Lantarki Da Sin Ta Samar Ya Karu Da Kaso 17.5%

October 26, 2025
Dalilin Da Suka Sa Hisbah Ta Dakatar Da Auren Ƴan TikTok A Kano

Dalilin Da Suka Sa Hisbah Ta Dakatar Da Auren Ƴan TikTok A Kano

October 26, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Gwarzon Ma’aikacin Gwamnati Na Shekarar 2025, Dakta Zacch Adedeji

October 26, 2025
An Yi Taron Tattaunawa Mai Taken “Shugabancin Duniya Da Samun Wadata Tare A Yankin Asiya Da Pasifik” A Beijing

An Yi Taron Tattaunawa Mai Taken “Shugabancin Duniya Da Samun Wadata Tare A Yankin Asiya Da Pasifik” A Beijing

October 26, 2025
Sin Da Amurka Sun Cimma Matsaya Dangane Da Tsare-Tsaren Warware Batutuwan Cinikayya Da Suke Mayar Da Hankali A Kai

Sin Da Amurka Sun Cimma Matsaya Dangane Da Tsare-Tsaren Warware Batutuwan Cinikayya Da Suke Mayar Da Hankali A Kai

October 26, 2025
Sharhi: Wannan Manufar Sin Za Ta Sa Kaimin Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya

Sharhi: Wannan Manufar Sin Za Ta Sa Kaimin Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya

October 26, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.