A ranar Asabar ne, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya gana da sakataren harkokin wajen kasar Amurka Antony Blinken a gefen taron ministocin harkokin wajen kasashen G20 a tsibirin Bali na kasar Indonesia.
Wang ya bayyana cewa, a halin yanzu, dangantakar dake tsakanin kasashen Sin da Amurka na cikin wani mawuyacin hali, wanda gwamnatin Amurka da ta shude ta haddasa, har ma tana kara fuskantar kalubale.
Babban dalili kuma shi ne, kasar Amurka tana da matsala game da yadda take kallon kasar Sin, kuma manufofinta game da kasar Sin sun kauce daga hanyar da ta dace.
Wang Yi ya jaddada cewa, tun da kasar Amurka ta yi alkawarin ba za ta nemi sauya tsarin kasar Sin ba, ya kamata ta mutunta tsarin gurguzu mai sigar musamman ta kasar Sin da jama’ar kasar Sin suka zaba, kana ta daina neman bata suna da takalar tsarin siyasa da manufofin cikin gida da waje na kasar Sin.
Tun da Amurka ta yi alkawarin cewa, ba za ta nemi tayar da wani “sabon yakin cacar baka ba”, to, ya kamata ta yi watsi da wannan tunani kwata-kwata. Tun da Amurka ta yi alkawarin ba za ta goyi bayan ‘yancin kai na yankin Taiwan ba, ya kamata ta daina neman yin illa da jirkita manufar Sin daya tak a duniya, da kuma daina fakewa da batun yankin Taiwan domin kawo cikas ga shirin sake dinkuwar kasar Sin cikin lumana. Tun da Amurka ta yi alkawarin cewa, ba ta da niyar tayar da wani rikici da kasar Sin, kamata ya yi ta mutunta iko da cikakkun yankunan kasar Sin, ta daina tsoma baki a harkokin cikin gidanta, da kuma kaucewa cin mutuncin halastacciyar moriyar kasar Sin ta hanyar fakewa da batun kare hakkin dan Adam da tsarin demokuradiyya.
Blinken ya gabatar da manufofin Amurka game da kasar Sin, yana mai cewa, Amurka ba ta neman tayar da wani sabon yaki cacar baka kan kasar Sin, ko sauya tsarin kasar Sin, da kalubalantar matsayin JKS, da yi wa kasar Sin kawanya, ko kuma goyon bayan ‘yancin kai na yankin Taiwan.
Amurka ta kuduri aniyar daidaita al’amurran da za su iya kawo cikas ga dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, kuma tana son yin hadin gwiwa tare da kasar Sin ba tare da wata rufa-rufa ba. (Ibrahim)