A cikin ’yan shekarun nan, a daidai lokacin da tattalin arzikin duniya yake durkushewa, ana samun karuwar kasashen Afirka wadanda suka amince da tattalin arzikin dijital a matsayin muhimmin ginshikin ci gabansu, kana alakar kasar Sin da Afirka ta sa kasar Sin zama babbar abokiyar hadin gwiwa wajen ciyar da tattalin arzikin dijital gaba a nahiyar Afirka da kuma cimma burinta na zamantarwa, a cewar Zhang Xiangchen, mataimakin darektan Hukumar Kasuwanci ta Duniya (WTO).
A cikin ’yan shekarun nan, bisa jagorancin wasu tsare-tsare irin su dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka, wato FOCAC da shirin shawarar “ziri daya da hanya daya”, yawancin kamfanonin kasar Sin na ci gaba da fadada zuba jari a Afirka.
A kasashe kamar Najeriya da Kenya, kamfanonin kasar Sin sun samar da tsarin biyan kudi ta wayar salula, tare da samar da amintattun hidimomi na biyan kudi na dijital ga miliyoyin masu amfani da tsarin. Bugu da kari, dandalin cinikayya na yanar gizo na kasar Sin yana baiwa jama’ar Afirka da dama damarmakin sayar da kayayyaki na musamman a duk duniya ba tare da barin gidajensu ba. (Mai fassara: Yahaya)