Hukumar yi wa kamfanoni rajista CAC ta shirya soke rajistar kamfanoni 91,843 saboda rashin bayar da rahoton ayyukansu na karshen shekara.
Hukumar ta bayyana haka ne a takardar da ta wallafa a shafinta na intanet, inda ta kara bayanin cewa, an shirya tsaf dson janye sunayen kamfanoni 91,843 daga kundin kanfanonin da ke harkokinsu a Nijeriya.
- An Gano Ciwon Ciki Da Ke Turnuke Sojojin Isra’ila A Gaza
- Kawancen Yakar APC: Jam’iyyun Adawa Sun Shiga Dimuwa
A watan Yuli, shugaban hukumar, Garba Abubakar, ya sanar da cewa, hukumar za ta soke sunanyen kamfanoni 100,000 daga safinsu na intanet saboda rashin cika ka’idar bayar da rahotonsu na shekara-shekara.
Ya kara da cewa, hukumar za ta aikewa kamfanonin takardar sanar da su shirin hukumar na janye sunayensu kafin a kai ga soke sunayen kamar yadda dokar kafa kamfanoni na sashi na 692 ya tanada.
A sanarwa da hukumar ta wallafa a ranar 5 ga watan Disamba, ta sanar da cewa, “Kamar yadda hukumar ta bayar da sanarwa a ranar 2 ga watan Agusta 2023, hukumar na sanar da al’umma cewa za ta soke sunayen dukkan kamfanonin da suka kasa cika sharuddan kawo rahoton ayyukansu kamar yadda dokar kafa kamfanoni na ‘Companies and Allied Matters Act 2020’ ya tanada.