Ministan wutar lantarki, Cif Adebayo Adelabu, ya ce da gangan aka cire aikin wutar Mambila a kasafin kudin ma’aikatar na shekarar 2024.
Adelabu wanda a ranar Litinin yake karin haske kan lamarin a lokacin da ya bay-yana a gaban hadakar kwamitin majalisar dattawa da na wakilai kan harkokin wu-ta da ke karkashin shugabancin Sanata Enyinnaya Abaribe.
Ya ce, aikin wutar Mambilla ya gamu da tarnakin shari’a a tsakanin gwamnatin tarayya da kamfanin ‘Sunrise Power and Transmission Company Limited (SPTCL)’ a ranar 10 ga watan Oktoban 2017, kan saba yarjejeniyar kwangila.
- EFCC Na Binciken Ba’asin Aikin Tashar Wutar Lantarki Ta Mambila – Minista
- Gwamnan Jihar Filato Zai Garzaya Kotun Ƙoli Don Ƙalubalantar Hukuncin Soke Zaɓensa
A yayin da gwamnatin take kare kanta kan karar da kamfanin ya shigar da ita, ta ce, aikin kwangilar bai kan ka’ida domin ba a bi dukkanin matakan da suka dace ba wajen bayar da shi.
Idan za a tuna dai, Dakta Olu Agunloye, ministan wuta a wancan lokacin ya bayar da kwangilar aikin kwana guda bayan da gwamnatin tarayya ta bukaci ya janye bukatarsa na bayar da amincewar kwangilar tare da lalubo hanyoyin samun kudin gudanar da aikin.
Kan hakan, kamfanin Sunrise ya garzaya kotu, kuma tun daga wancan lokacin wasu karin kararraki ma suka hana aikin ci gaba da gudana.
Ministan ya shaida wa ‘yan majalisan cewa, da saninsu suka cire aikin kwata-kwata daga cikin kasafin kudin shekara mai zuwa.
“Babu wani tanadi da aka yi wa aikin Mambilla a kasafin kudin 2024. Kuma hakan ba wai kuskure ba ne da saninmu da gangan muka yi hakan. Bisa yarjejeniyar kasa da kasa. Har sai an shawo kan lamura, ba za mu iya komai a kan aikin ba.”
Da yake magana kan aikin wutar Zungeru Hydro Power Project, ministan ya ce aikin ya ma kusa kammaluwa a halin da ake ciki.