Shafin TASKIRA, shafi ne dake zakulo muku batutuwa daban-daban wadanda suka shafi al’umma. A yau ma shafin na tafe da wani tsokacin daya shafi matasa ‘yan soyayya.
Da yawan ‘yan mata na fuskantar kalubale wajen samarinsu ta fannin yaudara, duk da cewa wannan tsokacin ba bakon shafin bane, sai dai mun samu sako daga wajen daya daga cikin mabiya shafin, inda ta bukaci a kara yin tsokaci game da wannan batu. Ta yadda mace take bawa namiji zuciyarta shi kadai bayan ta amince masa tare da tabbatar masa cewa babu wani da namiji da take son aura face shi daya tilo, yayin da wani saurayin ma zai je ya ga iyaye har a bashi izini, daga bisani kuma a neme shi a rasa, karshe sai dai a ji labarin ya auri wata ba ita ba, bayan ya gama bata mata lokaci, wata ma inda tsautsayi har rayuwarta ya gama batawa.
Dalilin hakan ya sa shafin TASKIRA jin ta bakin wasu daga cikin ma’abota shafin game da wannan batu; “Ko me yake janyo yawaitar afkuwar hakan a wannan lokaci? Ta wacce hanya ce mace za ta iya gane irin wadannan samarin, har ta iya kaurace musu ba tare da ta fada tarkonsu ba?, Idan mace ta ci karo da irin wannan mazan wanne mataki ya kamata ta bi?.
Ga dai ra’ayoyin nasu kamar haka:
Sunana Zainab Abdullahi (Laila), Jihar Katsina:
Da farko ya kamata mu san ma’anar ita kanta yaudarar, kafin sanin abin da ke kawo ta. Ma’anar yaudara dai ita ce; mutum ya nuna wata manufa, ko siffa a zahiri wadda ba ita ce a cikin zuciyarsa ba, domin biyan bukatar kansa, wanda hakan kan iya zama cutarwa ga wanda aka yibwa. Dalilai da yawa na kawo yaudara, amma ma fi girmansu shi ne jahilci da karancin tsoron Allah, domin yaudara babbar bala’i ce, tana cikin manyan zunubbai, kuma babu wani mutum da zai yi yaudara face ya aikata wadannan zunubban gaba daya; Karya, Cin Amana, Butulci, Ha’inci, Rantsuwa akan karya, Karya alƙawali. Mu ji tsoron Allah mu kiyaye kanmu daga yaudarar wani domin gudun kada mu ma a yaudare mu, don abin da duk ka yi wa wani sai an yi maka komai daren dadewa, kuma idan ma ka yaudari ‘yar wani kana tunanin kaci bulus anan duniya to fa kayi sauri ka canza tunani, domin Allah ba azzalumin bawa bane, sai fa wanda ya zalunci kansa, za ka mutu kuma Allah zai tuhume ka akan abin da ka aikata. Hanyar kare kanmu daga irin wadannan mazan ita ce; Ki zama mai yawaita addu’a, kada ki nuna maitar so ga saurayi koda kuwa ya kawo kudin aurenki gidanku, kada ki yaudari wani ko kadan, idan saurayi ya zo gare ki da batun soyayya kada ki amince masa farat daya, ki ba shi sati daya ko fiye da haka, kafin nan sai ki yi istikhara akansa, idan har mayaudari ne in sha Allahu Allah ba zai ba shi damar sake zuwa inda ki ke ba. Allah ya tsare mu yaudarar wasu, ya kuma hana wasu yaudararmu.
Sunana Aminu Adamu Malam Maduri A Jahar Jigawa:
To magana ta gaskiya wannan al’amari yana faruwa ta kowane bangare ba wai maza bane kadai suke yaudara, domin lokuta da dama ana samun matan su ma masu halin yaudara, kuma wasu lokutan ana fara soyayyar tsakani da Allah yana son ta tsakani da Allah tana son shi tsakani da Allah to amma yanayi na rayuwa ya raba su ma’ana rashin abun yi ko kuma matsalar rashin fahimta ta shiga tsakaninsu. To magana ta gaskiya gane mayaudarin saurayi abun-da kamar wuya a wannan hali da’ake ciki domin wani zai bi dukkanin wasu matakai na neman aure da shari’a ta gindaya kafin ya zo neman aurenki to, amma kuma bada gaske yake ba, don haka mafita anan ita ce addu’ar Allah ya baki miji nagari sai ki ga an dace. Matakin daya kamata ta dauka shi ne kada ta basu dama tayi kokarin nesanta kanta da su duk dabaru ko salo da za su zo da su ta kauce musu ta kuma dage da addu’ar Allah ya kare ta daga dukkanin samari mayaudara, kuma ita tayi kokarin kaucewa yaudarar wasu mazan domin a wasu lokutan “kaikayi ne yake koma wa kan mashekiya”, wannan ita ce gaskiyar magana. Shawarar da zan basu ita ce; su dage da addu’ar Allah ya basu samari nagari masu tarbiyya ta addini da kuma ilimin zamani, kuma su ma kada suyi kokarin yaudarar wasu samarin duk lokacin da wani ya zo gurinsu kuma ba su aminta da shi ba to su fadi gaskiyar lamari ba wai suna tatse shi ba kuma ba son shi ake ba, daga karshe nake addu’ar Allah ya hada dukkanin mai kyakkyawar manufa da irinsa.
Sunana Bilkisu Muhammad salis, Jihar kano:
Laifin iyaye ne musamman duba ga Al’adar malam bahaushe. Akwai kunya tsakanin iyaye da ‘yayansu wanda hakan ke cutar da su yaran bayan sun girma, kamata yayi ace yarinya tun tana karama ana sanyata wasu ayyukan gidan adadin shekarunta adadin karuwar aikinta kamin farga za a ga duk ta saba. Ita uwa ita ce jigon da za ta na zaunar da ‘yarta tana koyar da ita dabarun zaman duniya. A gaskiya kamata yayi, ya nema mata makaranta ya sata, musamman ma matan aure dana girke-girke. Shawarata ga iyaye su rage kunya tsakaninsu da ‘ya’yansu su koya musu abin da ya dace duk abin da ya danganci mijin, iyaye su zama abokan ‘ya’yansu ta yadda za su san matsalolinsu, sannan shawarata ga ‘yan mata a dinga kula da kai da kuma dinga bin shafikan koyan girke-girke da kwalliya domin karin basiru.
Sunana Lawan Isma’il (Lisary), Jihar Kano, Karamar Hukuma Rano:
Abin da yake jawo irin wannan shi ne; son kai da son zuciya da rashin tunanin me zai je ya dawo, domin duk abin da kayi ka sani sai an yi maka ko wani naka mace ko namiji. Hanyoyin magancewa akwaisu da yawa, amma ga wata daga ciki; Da zarar kin ji a ranki kin aminta da shi a matsayin wanda za ki aura to tashin farko ki ce ya zo gidanku su gaisa da iyayenki, sannan ki sanarwa da iyayenki ko wani nakusa dake wanda zai iya sanar da su. Sabida ana samun wasu ‘yan matan da jin kunyar iyaye ace da su kin sami wanda ki ke so, kuma kin ce ya zo su gaisa. Su kuma iyayenki su sakashi ya turo nasa iyayen duk abin da zai biyo baya kuma a jira hukuncin da Allah zai yi. Matakin da ya kamata ta dauka kusan wanda na ce ne a maganata ta 2, karin hasken kawai da zan yi shi ne; idan tayi kokarin gabatar da shi ga manyanta ta ga yana kwalo-kwalo ko kuma ta tabbatar da ya hadata da nasa manyan bana gaskiya ba to kawai ta fita sabgarsa ta ma daina bashi fuska domin akwai samari ko ‘yan mata masu dakko iyayen karya domin samun zldamar yaudarar juna. Shawarata anan na farko shu ne; Addu’a da neman zabin ubangiji sannan ke ma kanki akwai gwajin da za ki iya yi wa saurayi, domin ki gane abokin zaman aurenki ne ko akasin hakan tun kafin tafiya tayi nisa.
Allah kasa mu dace. Abin da ke jawo hakan shi ne sabawa ko kuma kaucewa yadda addini ya tsara a nemi aure, ya kasance kawai saurayi zai ga budurwa a hanya ko ta kafar sadarwa ko ta silar wata kawa shikenan kawai sai ita yarinya ko nace budurwa ta amince masa dari bisa dari ayi ta soyayya wacce kashi casa’in cikin dari duk karya ce. Hanyar magancewa guda daya ce, ita ce; hanyar da addininmu na musulunci da kuma tarbiyya ta musulunci ta koyar da mu wato ya kasance ayi haduwa ta mutunci idan saurayi ya ga budurwa maimakon ya fara yi mata magana, sai ko ya fara neman iznin yi mata magana daga magabatanta, matukar za a yi hakan in sha Allahu za a kauce wa duk wata barna. Da zarar mace ta gano irin wannan namijin mara gaskiya da Amana tayi gaggawar rabuwa da shi wannan ita ce gaskiyar magana. Shawara ita ce su ji tsoron Allah SWT su bi dokoki da iyakoki da aka shimfida a neman aure su tsare mutuncinsu wannan shi ne kawai.
Sunana Daniel G Abarshi, Tabawa Balewa Jihar Bauchi:
To magana ta gaskiya shi ne yawan kwadayi da san kudi da mata suke da shi ya kan janyo musu yaudara. To gaskiya idan har mace ta zama ta gari takan yi addu’a Allah ya bata miji nagari, ya kamata ki san asalinsa, iliminsa, kadan daga tarihin rayuwarsa da kuma tarbiyyar gidansu da ma tashi tarbiyyar. To magana ta gaskiya shi ne duk wanda ya yaudareka ko baka ce komai ba, da akwai hakki Allah ma ba zai barsa ba, ta bar shi da Allah shi yafi. Magana ta gaskiya shi ne su rinka son mutum don Allah su rage san kudi da abin duniya, sannan su yi buncike akansa kafin su yi zirfi a soyyayarsa wannan shi ne shawara.