Assalamu Alaikum. Malam na kasance ina kyautata wa mijina iya gwargwadona, to amma matsalar ba ni kadai ba ce sai yakasance ni ma yana mun duk wani abu na jin dadi da kyautatawa fiye da kishiyar tawa wani lokacin ma ba ya boyewa, to shin malam ba ma shiga hakkinta. Mene ne hukuncin haka? Na gode.
Wa alaikum assalam. Ya wajaba ayi adalci a lamura na zahiri (kamar abinci, tufa) tsakanin kishiyoyi, Annabi (SAW) yana cewa: “Duk Wanda yake da mata biyu, amma bai yi adalci a tsakaninsu ba, zai zo ranar alkiyama sashensa daya a shagide”.
Ya halatta in kana da mata guda biyu ka fi son daya daga ciki, ka fi jin dadin saduwa da ita, ka fi dadewa a dakinta, Annabi (SAW) ya fi son nana Aisha a kan duka matansa tara da ya mutu ya bari, kuma matansa da sahabbansa sun san hakan, kamar yadda ya tabbata a sahihul Bukhari.
Allah ne mafi sani.